Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya raba tallafin naira miliyan 102 ga matasa 102 da suka kammala samun horo a cibiyar noma ta Songhai da ke ƙaramar hukumar Dutsinma a Jihar Katsina.
Kowanne ɗalibi daga cikin ƙananan hukumomin 34 ya samu naira miliyan ɗaya a matsayin jari, bayan sun kammala samun horo na watanni shida.
Sun sami horo a ɓangaren kiwon kaji, kifi, noma, sarrafa ƙasa, kiwon dabbobi, lambu da fasahar samar da iskar gas daga shara.
A jawabin sa wajen taron, Gwamna Raɗɗa ya bayyana shirin a matsayin “juyin juya hali a tarihin noma na jihar Katsina.” Ya jero wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar, ciki har da shirin noman damina na 2023, rabon kayan aikin noma da rangwame, da kuma shirin zamani na injinan noma wanda ya haɗa da rabon taraktoci, injinan ban ruwa, da takin zamani a farashi mai sauƙi.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa zagayen gaba na shirin Songhai zai horar da mutum 361 ɗaya daga kowanne yanki na jihar don tabbatar da shigar al’umma daga ƙasa har sama.
Malam Dikko Raɗɗa ya yi alƙawarin ci gaba da zuba jari a fannin noma, samar da wutar lantarki da kuma bunƙasa auduga, tare da mayar da hankali wajen ɗaukar matasa aiki, rage talauci da ƙara samar da abinci.
Kwamishinan ma’aikatar noma, Farfesa Ahmed Bakori, ya bayyana bikin a matsayin sabon babi ga noma a Jihar Katsina, yayin da mataimakin shugaban ALGON na jihar, Rabo Tambaya, da shugaban marasa rinjaye na majalisar dokoki, Hon. Shamsudeen Abubakar Dabai, suka tabbatar da goyon bayan shugabannin ƙananan hukumomi da ‘yan majalisa.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka samu horo Umar Mukhtar ya yi alƙawarin amfani da ilimin da suka samu wajen ƙara samar da abinci da inganta ci gaban jihar.
