Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Shugaban hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta NECO, Farfesa Ibrahim Wushishi ne ya bayyana haka a garin Minna babban birnin jihar Neja yayin da yake sanar da sakamakon jarrabawar ta wannan shekara ta 2025.
Farfesa Wushishi ya ce ɗalibai 68,159 ne suka samu kiredit biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi daga Jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sai Jihar Legas da ke biye mata da ɗalibai 67,007, a inda Jihar Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 48,742.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga matakan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka wajen farfaɗo da ilimi, da suka haɗar da ware kaso 31% na kasafin kuɗin jihar ga ɓangaren ilimi da ɗaukar malamai da gyaran makarantu, da samar da kayan koyo da koyarwa kyauta.
Sanarwar ta ƙara da cewa nasarar ta biyo bayan jajircewar gwamnatin jihar Kano wajen inganta ilimin ‘ya’ya mata da rage yawan yaran da basa zuwa makarantar da gyara makarantu da kuma inganta walwalar malamai.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa bisa wannan nasara, yana mai cewa kwalliya ta biyan kuɗin sabulu.
Wannan nasara na zuwa duk da irin rahotanni da wasu ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa irinsu UNICEF ke fitarwa na koma bayan ilimi a jihohi na Arewacin Najeriya.
