Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan ya jaddada cewa dole ne a yi amfani da duk hanyoyin sadarwa da ake da su—rediyo, talabijin, kafafen sada zumunta, da tarukan al’umma—don isar da saƙon ga maniyyata a faɗin jihar domin su fara rajistar aikin hajji da wuri.
Haka kuma ya roƙi malamai su yi amfani da huɗubobinsu da karatuttukansu wajen tunatar da al’umma a masallatai kan buƙatar yin rajista da wuri.
Gwamna Raɗɗa ya bayar da wannan umarni ne lokacin da ya karɓi shugaban hukumar hajji na ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman Saleh Pakistan, wanda ya jagoranci tawagar manyan jami’an hukumar a ziyarar ban girma zuwa fadar gwamnati ta Jihar Katsina.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana matuƙar jin daɗin sa ga jajircewar hukumar wajen inganta jin daɗin alhazan Najeriya.
Ya tabbatar wa tawagar NAHCON cewa Jihar Katsina za ta bayar da cikakken goyon baya ga duk wani shiri da zai sauƙaƙa gudanar da aikin Hajji.
Gwamnan ya kuma yaba wa hukumar kan yadda take kula da tsafta da inganci a ayyukanta, inda ya yi alƙawarin isar da matsalolin hukumar ga taron Gwamnonin Arewa maso Yamma, wanda shi ne shugaban ƙungiyar.
Haka kuma ya shawarci hukumar da ta ƙarfafa alaƙarta da gwamnonin yankin domin samun cikakken goyon baya ga ayyukanta.
A nasa jawabin, Farfesa Abdullahi Usman Saleh Pakistan ya bayyana cewa manufar ziyararsa ita ce ya sanar da Gwamna Raɗɗa, a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma, kan muhimmancin fara shirin wayar da kai da kuma tattaunawa da maniyyata tun da wuri domin aikin Hajjin 2026.
Shugaban NAHCON ya jaddada cewa biyan kuɗin ajiya da wuri daga maniyyata zai bai wa jihohi damar samun gidajen kwana masu kyau kusa da Masallatan Harami a Makka da Madina.
Ya bayyana cewa jinkirin biyan kuɗin a shekarun baya ya jawo cikas wajen samun wuraren da suka dace ga maniyyata.
Farfesa Pakistan ya nuna damuwarsa kan matsalolin da ake fuskanta sanadiyyar jinkirin rajista, inda ya jaddada cewa shirin tun da wuri ne kaɗai zai tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi.
Haka kuma ya roƙi Gwamna Raɗɗa da ya isar da godiyar hukumar ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa sakin kuɗaɗe a kan lokaci, wanda ya taimaka matuƙa wajen inganta shirye-shiryen hukumar don aikin Hajji.
Shugaban NAHCON ya samu rakiyar manyan jami’an hukumar a ziyarar, yayin da daga ɓangaren gwamnatin jihar akwai mataimakin gwamnan Katsina, Malam Faruk Lawal Joɓe, shugaban ma’aikata na Fadar Gwamnati, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Isiaq Shehu Dabai, Mataimakin Shugaban Ma’aikata, Muntari Aliyu Saulawa, da kuma Shugaban da Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar, Alhaji Kabiru Ibrahim (Sarkin Alhazai) da Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama.
