Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A watan Maris ɗin 2025 ne Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas bayan ya bayyana cewa rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da majalisar dokoki ya jawo “durƙushewar mulki gaba ɗaya.”
Tinubu ya ce, rikicin ya taɓa manyan kadarorin tattalin arzikin jihar, musamman bututun mai da ake lalatawa, abin da ya sanya dole ya dakatar da gwamnati da majalisar dokoki na tsawon watanni shida.
A lokacin, ya naɗa tsohon shugaban sojojin ruwa, ɓice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), a matsayin shugaban riƙon ƙwarya domin tafiyar da jihar mai arzikin mai.
Shugaba Bola Tinubu ya ce, ya janye dokar ta baci a jihar Riɓers bayan an samu haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki.
Fubara wanda ya gaji Nyesom Wike, ya shiga rikici da magabacinsa kasa da shekaru biyu a ofis, kan ikon sarrafa jam’iyyar PDP da tsarin siyasa a jihar.
Wannan rikici ya ratsa har majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule, abin da ya tilasta wa Tinubu yin katsalandan bisa tanadin Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki na 1999.
A sabon jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya ce bincike ya nuna cewa an samu sabuwar fahimta a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a Ribas domin komawa tafarkin dimokuraɗuyya cikin gaggawa.
Shugaban ƙasar ya gode wa sarakunan gargajiya da al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka bayar daga lokacin da aka kafa dokar har zuwa ƙarewarta.
Yayin da ya ke kare matakin da ya ɗauka na ƙaƙaba dokar ta-ɓacin, Shugaba Tinubu ya tunatar da gwamnonin jihohi da majalisun dokokin ƙasar daftarin tsarin mulkin da ya bai wa Gwamnatin Tarayya ikon kafa dokar ta-ɓaci inda zaman lafiyar al’umma ke fuskantar barazana.
Tinubu, a wani jawabi da ya yi a ranar Laraba, ya ce, tanade-tanaden tsarin mulki ne da aka tsara don maido da zaman lafiya da kuma tsaro ya sa aka saka dokar ta-ɓacin.
“Ikon ayyana dokar ta-ɓaci wani tsarin mulki ne da aka gina don magance al’amura na zahiri ko barazanar rugujewar zaman lafiyar jama’a da amincin jama’a, waɗanda ke buƙatar tsauraran matakan dawo da jihar cikin zaman lafiya da tsaro,” inji shugaban.
Ya ƙara da cewa, dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas bai kasance ba tare da adawa ba, yana mai cewa wasu ‘yan ƙasar da ƙungiyoyi sun ƙalubalanci hukuncin a gaban kotu.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma bayyana cewa, an shigar da ƙararraki fiye da 40 a kotu a jihohi uku na ƙalubalantar kafa dokar ta-ɓaci a jihar Ribas.
Ya bayyana cewa daga bayanan sirrin da ake da shi, an samu sabon tsari mai ƙarfi da kuma kwarin gwiwa daga ɓangaren masu ruwa da tsaki a jihar Ribas domin dawo da mulkin dimokraɗiyya cikin gaggawa”.
Wannan, a cewarsa, ko shakka babu abin farin ciki ne a gare shi, kuma wani gagarumin nasara ce ga ƙasar.
Yayin da ya ke ƙarin haske game da cece-kucen da ya biyo bayan matakin nasa, Tinubu ya bayyana cewa an shigar da ƙararraki fiye da 40 a kotu a jihohi uku na ƙalubalantar kafa dokar ta-ɓaci da ya yi.
Ya bayyana cewa an shigar da ƙararrakin ne a kotunan Abuja, Fatakwal, da Yenagoa, jihar Bayelsa, waɗanda ke adawa da wannan mataki. Ya yi nuni da cewa, duk da cewa rashin amincewa ya zama ɗabi’a a tsarin dimokuraɗiyya, al’amuran da ke faruwa a Ribas sun sa ba shi da zaɓi.
“Haka ya kamata ya kasance a cikin tsarin dimokuraɗiyya, wasu shari’o’in har yanzu suna kan gaban kotuna har zuwa yau. Amma abin da ya kamata a ce shi ne ikon ayyana dokar ta-ɓaci wani mataki ne na tsarin mulki da aka gina don magance al’amura na zahiri ko kuma barazanar rugujewar zaman lafiyar jama’a da amincin jama’a, “inji shugaban.
Tinubu ya jaddada cewa, hukuncin da kotun koli ta yanke kan rikicin da ke tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisar dokokin jihar Ribas ne ya jagoranci yanke hukuncin, wanda ya yi nuni da girman rashin zaman lafiya a jihar.
Shugaban ya ƙara jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsakanin ɓangaren zartaswa da na majalisar dokoki a matakin jihohi da na aasa baki ɗaya, yana mai cewa irin wannan haɗin kai na da muhimmanci wajen samar da shugabanci na gari.
Shugaban ya buƙaci shugabannin siyasa a matakin jiha da su yi aiki tare da sanin ya kamata, yana mai jaddada cewa shugabanci nagari ba zai samu ba sai a yanayin zaman lafiya.
“Ina amfani da wannan dama wajen tunatar da Gwamnoni da Majalisun Dokoki na Jihohin ƙasarmu da su ci gaba da fahimtar cewa a cikin yanayi na zaman lafiya, tsari, da gwamnati mai kyau ne kawai za mu iya isar da ribar dimokuradiyya ga al’ummarmu. Ina roƙon dukkan ku da ku bar wannan fahimtar ta motsa ayyukanku a kowane lokaci,” inji Tinubu.
Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) ya miƙa ragamar mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Sim Fubara. An bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin watsa shirye-shiryen ƙarshe a faɗin jihar ta bakin mai gudanarwa.
A watan Maris ne dai shugaba Bola Tinubu ya kafa dokar ta-baci a Ribas tare da dakatar da Fubara da mataimakinsa Ngozi Odu da dukkan zaɓaɓɓun ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.
Ya ci gaba da naɗa ɓice Admiral Ibas mai ritaya a matsayin mai kula da harkokin mulki na jihar.
Sai dai shugaban ya ɗage dokar ta-ɓacin tare da mayar da Fubara bakin aiki a ranar Laraba 17 ga watan Satumba.
Yayin da ya ke jawabi yayin miƙa mulki, Ibas ya yi iƙirarin cewa ya samu nasarar maido da doka da oda a jihar mai arzikin man fetur.
Ya buƙaci al’ummar jihar da su marawa Fubara baya domin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na jagorancin jihar.
Ibas ya ce; “Ya ku ‘yan uwa na Jihar Ribas, tare da godiya a cikin zuciyata, ina yi muku jawabi a yau a karo na ƙarshe a matsayin mai kula da jiharmu.
Sai dai kuma, Majalisar Dokokin jihar ta Ribas ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen jihar a lokacin dokar ta-ɓacin watanni shiga.
Idan baku mana ba, Ibok-Ete Ibas ya yi mulki na tsawon watanni shida a matsayin shugaban riko na jihar Ribas bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.
An tattaro cewa bayan cire dokar, Majalisar Dokokin jihar Ribas ta koma aiki a ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
A zaman farko da Majalisar ta gudanar, ta cimma matsayar gudanar da bincike kan yadda shugaban riƙo ya tafiyar da dukiyar jihar Ribas a tsawon watanni shida.
Haka kuma, majalisar ta buƙaci gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ya aika da jerin sunayen waɗanda ya zaɓa a matsayin kwamishinoni domin tantancewa da amincewa.
Tun a ranar, watau 17 ga Satumba, 2025 ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wanda hakan ya dawo da dukkan tsarin dimokuraɗiyya a jihar Ribas.
Kakakin majalisar, Rt. Hon. Martins Amaewhule, ne ya jagoranci zaman a ɗakin taro da ke cikin harabar majalisar, wadda har yanzu ake kan aikin gina ta.
Hakan dai ya faru ne sakamakon rusa tsohuwar majalisar da gwamnatin jihar Ribas ƙarƙashin Gwamna Fubara ta yi a baya lokacin rikicin siyasa.
Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun mamaye ƙofar Fadar Gwamnati da ke Fatakwal, domin tarbar sa. Cikin magoya bayan gwamnan akwai manyan jiga-jigai da tsofaffin mambobi na tsohuwar ƙungiyar Simplified Moɓement, wacce aka rushe ta daga baya.
Daga cikinsu akwai tsohon Kakakin majalisar dokokin mutum uku da aka rusa, ɓictor Oko-Jumbo, wanda ya jagoranci wasu wajen jiran gwamnan.
Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan gwamnan sun fito daga sassa daban-daban na kananan hukumomi 23 na jihar Ribas domin tarbar dawowarsa a Fatakwal.
Wani daga cikinsu ya bayyana cewa sun zo ne su tarbi mai girma gwamna yayin da zai koma kan mulki, wanda dama hakkinsa ne.
ɗaruruwan masoya da masu fatan alheri na ci gaba da tururuwar zuwa ƙofar shiga gidan gwamnatin Ribas da ke Fatakwal da safiyar yau Alhamis.
Sai dai har kawo yanzu ba a tabbatar da lokacin isowar gwamnan ba, haka kuma ba a san ko zai tsaya a kofar wajen ya yi magana da su ba kafin ya shiga ofis.
An ga mata sanye da kayan ado masu launi-launi, ƙungiyoyin raye-raye, matasa da wasu dattawa a cikin yanayi na murna yayin da suke jiran zuwansa.
Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya cire dokar ta-ɓacin da ya sanya a jihar Ribas watanni shidada da suka gabata.
Shugaba Tinubu ya sanar da cewa dokar za ta kare a ƙarshen ranar Talata, sannan ya umarci Gwamna Fubara da ’yan Majalisar Dokokin Ribas su koma aiki yau Alhamis.
Cire dokar ta-ɓacin ya ja hankalin masu ruwa da tsaki da manyan jiga-jigai a ƙasar nan, inda wasu ke nuna farin cikinsu da ci gaban da aka samu a jihar Ribas, wasu kuma na suka.
A halin yanzu dai magoya bayan Fubara sun kewaye gidan gwammati da ke Fatakwal, suna dakon isowar mai girma gwamna.
Duk da dandazon jama’a, ba su ga gwamna ba: Magoya bayan Fubara sun fita cikin ɓacin rai:
Jama’an da suka yi cincirando don ganin Fubara, sun tafi cikin ɓacin rai bayan sun gaza ganin sa a fili.
An rawaito cewa dandazon ma’abota kishin ƙasa sun taru a ƙofar gidan gwamnati da misalin ƙarfe 6:00 na safe, inda wasu suka taho daga sassan jihar.
Sun zo ne domin tarbar gwamnan bayan ɗage dokar ta-ɓaci ta tsawon watanni shida da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a hukumance, matakin da mutane da yawa ke kallon a matsayin nasara a siyasance ga Fubara bayan shafe tsawon watanni ana gwabza ƙazamin faɗa da wani ɓangaren majalisar dokokin jihar da ke biyayya ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.
Sama da sa’o’i shida, magoya bayan da suka haɗa da matasa, ƙungiyoyin mata, da ‘yan siyasa, suna jira da rana a wajen gidan gwamnati, suna rera waƙoƙin haɗin kai da kuma fatan ganin gwamnan.
Da tsakar rana, takaici ya fara tashi. Da 12:00 na rana – 1:00 na rana, da yawa sun fara watsewa bayan da ba a samu labarin zuwan gwamnan a hukumance ba.
Wasu jiga-jigan siyasa da suka haɗa da tsohon shugaban Obio/Akpor LG, Chijoke Ihunwo, da kuma tsohon shugaban LG City na Port Harcourt, Ezebunwo Itche-Mati, an gansu suna ta waya, suna ƙoƙarin tabbatar da motsin gwamnan. Zuwa ƙarfe 3:00 na yamma har yanzu ba a san inda yake ba.
Magoya bayan da dama, waɗanda a bayyane suke cikin ɓacin rai, sun bayyana rashin jin daɗinsu ga manema labarai.
Majalisar Dokokin jihar Ribas ta dawo da zama a karon farko bayan Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci. ’Yan majalisar dokokin jihar Ribas sun dawo da zamansu na majalisa da ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025.
Dawo da zaman majalisar na zuwa ne ‘yan awanni kaɗan bayan sanarwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye dokar ta-baci a jihar.
An ruwaito cewa majalisar, ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisa, Hon. Martin Amaewhule, za ta fara zama a rukunin gidajen majalisar da ke kan hanyar Aba–Port Harcourt.
Rahotanni sun nuna cewa mambobin majalisar guda 27 sun isa jihar kwanaki kafin ƙarewar dokar ta-ɓaci, kuma yanzu haka sun shirya fara zamansu na farko.
Ya zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, an ce ‘yan majalisa, masu zama a rukunin gidajen majalisar sun riga da sun fara haduwa don fara zaman.
PDP ta gargaɗi Fubara kan komawa APC saboda ɗaga dokar ta-ɓaci a jiharsa:
Sai dai kuma babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya kuma wacce Fubara ya ke mambanta ne, wato PDP, ta yi kakkausan kira ga Gwamna Siminalayi Fubara da ya ci gaba da yi wa jam’iyyar biyayya, ya yi watsi da zarge-zargen da jam’iyyar APC ta yi masa tare da ƙaddamar da cikakken bincike kan yadda aka gudanar da mulkin Jihar Ribas a lokacin da ba ya nan, sannan kuma kada ya kuskurra ya koma cikin APC bisa kowacce irin barazana.
Biyo bayan dawowar Fubara kan karagar mulki a ranar Alhamis, jam’iyyar APC a matakin jiha da ta ƙasa a jiya ta buƙaci gwamnan da aka dakatar ya bar jam’iyyar PDP, ya kafa sansani a cikin APC.
Da yake magana da jaridar DailyTrust a wata hira, Daraktan Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya ce, sauya sheƙar Fubara zuwa APC zai ƙara wa jam’iyya mai mulki cigaba.
Ya bayyana cewa manufar jam’iyyar APC ba wai kawai ta lashe jihar Ribas ne a shekarar 2027 ba, a’a, domin ta mallaki dukkanin jihohin ƙasar nan 36.
