Ba iya gwamna ba, har takara da mahaifinsa a kujerar shugaban ƙasa Seyi Tinubu ya cancanci yi – Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Fadar Shugaban ƙasa ta bakin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu Shawara kan Harkokin Sadarwa da Tsare-Tsare, Daniel Bwala, ya yi watsi da masu suka kan ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, bisa raɗe-raɗen cewa zai tsaya takarar gwamnan jihar Lagas.

Bawla ya bayyana cewa ko da yake Seyi bai fito fili ya bayyana muradinsa na tsayawa takarar ba, babu wata doka da ta hana shi neman wannan kujerar ta gwamna.

Da yake magana a shirin The Clarity Zone Podcast, Bwala ya bayyana cewa matsayin mahaifin Seyi a shugaban ƙasa bai kamata ya zama dalili na hana shi tsayawa takara ba domin babu dokar da hana shi yin haka, har ma ga kujerar shugaban ƙasa idan yana so.

“Seyi har ma yana da ƴancin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 idan yana so ya ƙalubalanci mahaifinsa a zaɓen shugaban ƙasa ba wani abu ba ne a dokar ƙasa”, inji shi.

Ya ƙara da cewa, Seyi tuni ya fara gina suna da tasiri a tsakanin matasa da al’umma, wanda hakan na iya zama haske ga makomarsa a siyasa.

Saidai kuma, akwai masu ganin babban ƙalubalen da zai fuskanta shi ne janyo ra’ayoyin jama’a da yadda za a fahimce shi, wato a matsayin ɗan da ya gaji daular siyasa, ko kuma matashi mai hangen nesa na kansa.

Wannan batu ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin dama ce ta matasa, wasu kuma na ganin ba daidai ba ne a cigaba da mulki cikin iyali.

By Babaji