Yobe: ‘Yan bindiga sun harbi ɗan sanda yayin hari a Sakatariyar NUJ

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A safiyar yau Juma’a wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa (NUJ) reshen Jihar Yobe da ke Damaturu, inda suka raunata wani ɗan sanda.

Lamarin da ya tada hankali musamman ga tsaron ƴan jarida a yankin Arewa maso Gabas.

Al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 2 na dare a lokacin da maharan suka kai hari a sakatariyar.

A yayin haka ne suka harbi ɗan sandan da ke gadi a farfajiyar sakatariyar a ƙafarsa.

Tuni aka garzaya da shi sashin gaggawa a Asibitin Ƴan Sanda da ke Damaturu, inda ake ba shi magani.

Shugaban NUJ na Yobe, Rajab Ismail Mohammed ya ce faruwar al’amarin ya yi sanadin jefa tsoro acikin ƴan jarida da ke aiki a jihar.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike a kai da tabbatar da an hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.

By Babaji