CERSDOV ta faɗaɗa yaƙi da cin zarafin mata a Akko da Billiri

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Cibiyar nazari da magance matsalolin cin zarafi a gida (CERSDOV) ta faɗaɗa wayar da kai kan ’yancin lafiyar haihuwa da yaƙi da cin zarafin mata zuwa ƙananan hukumomin Akko da Billiri a Jihar Gombe, tare da tallafin gwamnatin Norway.

A yayin taro da ƙungiyoyin mata a Kumo, babban mai bincike na CERSDOV, Dokta Hussaini Momoh Lawal, ya ce ziyartar na nufin duba tasirin horon da aka gudanar a matakin al’umma, tare da ƙarfafa mata su karya shingayen al’ada domin kare kansu da ’yan mata masu tasowa.

Jakadiyar CERSDOV wacce kuma lauya ce a ma’aikatar shari’a ta Jihar Gombe, Mwalin Naomi Abdu, ta jaddada cewa dole ne iyaye, gwamnati da shugabannin addini da na gargajiya su taka rawa wajen kawo ƙarshen cin zarafi.

A Akko, jakadun da aka horar sun ce shirin ya ƙarfafa musu fahimta wajen magance matsalolin GBV da SRHR, kana suna ci gaba da tattaunawa da mata da ’yan mata don taimaka musu su zama masu dogaro da kai.

Shugaban da’awa na Akko, Mamman Alhaji Buba, da Shugaban CAN na Akko, Fasto Barnabas Yakubu Faruq, sun yaba da shirin tare da kiran ƙarin shiga daga maza da shugabannin al’umma.

A Billiri kuwa, mata sun bayyana cewa adadin ƙararrakin fyaɗe da cin zarafi ya ragu, suna danganta hakan da wayar da kai da kuma faɗakarwar da CERSDOV ke gudanarwa.

By ukarofi