Sanata Marafa ya bar APC ne saboda gazawar Shugaba Tinubu – Maikatako

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

An bayyana ficewar Sanata Kabiru Garba Marafa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara a baya-bayan nan, ya biyo bayan gazawar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen sa, musamman alƙawarin da ya yi na kawo ƙarshen rashin tsaro da ya addabi jihar.

Alhaji Surajo Garba Maikatako, Shugaban Majalisar ƙoli ta ƙungiyar Sanata Marafa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau yau Juma’a.

Ya ci gaba da cewa, ficewar Sanata Kabiru Garba Marafa daga jam’iyyar APC a Zamfara a baya-bayan nan ta sake dawo da martabar siyasarsa.

Maikatako ya ƙara tabbatar da furucin da Sanata Marafa ya yi da kakkausar murya, cewar za su cire kasa da ƙuri’u miliyan ɗaya daga ƙididdigar da shugaban ƙasa zai samu a zaɓe mai zuwa.

A cewarsa, ficewar Sanata Kabiru Garba Marafa daga APC ya saɓawa yadda wasu ke zato, ganin cewa hakan alheri ne da za a kawo sauyi a tafiyarsa ta siyasa.

“Na sha samun ɗimbin kiraye-kiraye da ziyarce-ziyarce daga magoya bayan sa a faɗin ƙasar nan – Arewa maso Yamma, Arewacin Najeriya, suna nuna goyon bayan ficewar sa daga APC Suna masu goyon bayan shirye-shiryen tafiya da Sanata Marafa zuwa mataki na gaba a siyasa”.

“Wannan ƙarin goyon bayan da aka samu ya nuna ƙarara farin jininsa da kwarjinin sa”.

Maikatako ya bayyana cewa Sanata Marafa zai cigaba da kasancewa ɗaya daga cikin jagororin siyasar zamani, irin ta masu hangen nesa, da rashin son kai, yana mai jaddada cewa APC a Zamfara ta mutu a siyasance.

Ya musanta zargin da APC ta yi na cewa sun karɓi ɗimbin magoya bayan Sanata Marafa, inda ya bayyana ikirarin da APC ta yi a matsayin soki burutsu.

“Mutanen da suka karɓa ba su kai adadin ƙuri’a ɗaya ba, duk da haka suna cigaba da ƙarawa miya gishiri da yaudarar jama’a, hakan ya bayyana rauninsu ne kawai a siyasance da firgicinsu”. Yace

“Jama’ar Zamfara kawai suna kallon shugabannin APC a matsayin huntaye a kasuwa, domin a maganar gaskiya babu jam’iyyar APC a jihar Zamfara “. Inji Maikatako

By ukarofi