
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƴan uwa da abokan arziƙi sun samu numfasawa bayan da ɗan majalisar dokokin Filato da ke wakiltar Pankshin ta Kudu, Laven Denty Jacob ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga kwanaki kaɗan da yin garkuwa da shi a jihar.
Da yake tabbatar da lamarin a ranar Laraba, Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Hon. Kwarpo Sylvanus, ya ce Hon. Jacob ya samu komawa wajen iyalansa cikin ƙoshin lafiya.
Ya bayyana cewa, an sako shi ne a daren Talata wayewar Laraba ya bayan ya bar hannun ƴan bindigar, saidai ba su da masaniyar ko an biya kuɗin fansa gabanin sako shi.
Ya kuma yaba wa jami’an tsaro da ɗaukacin al’umma bisa hoɓɓasa da gudumawar addu’o’i da suka yi wajen ganin an yi nasarar ceto shi.
Sylvanus har’ilayau, ya yi kira ga mazauna yankuna da su cigaba da sanya ido akan ababen da ke kai kawo tare da aika wa hukuma rahoton dukkan wani abin zargi, yana mai cewa za su cigaba da ƙoƙarin ganin an samar da dokokin tsaro masu ƙarfi domin bunƙasa harkar a jihar.
Kazalika, ya nemi a kafa jami’an bijilante domin taimaka wa ayyukan jami’an tsaro a Filato.
