Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Legas ta fara rusa wasu gidaje marasa aminci a harabar Kasuwar Baje Kolin Duniya da ke Ojo.
Ma’aikatar Tsare-tsare, Hukumar Kula da Gine-gine da Hukumar Sabunta Birane da Hukumar Bada Izinin Tsara Gine-gine na jihar ta Legas ne suka gudanar da aikin a tare cikin aiki na haɗin gwiwa.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin kafafen yaɗa labarai ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Jubril Gawat, ya tabbatar da wannan aiki a wani saƙo a shafin ɗ.
A cewarsa, an ɗauki matakin ne domin dawo da oda da kuma aiwatar da dokokin tsare-tsaren gine-gine.
Ya ce, aikin an yi niyya ne kan daƙile gine-gine ba bisa ƙa’ida ba, gine-gine ba tare da amincewar doka ba, nakasassun gine-gine, da gine-ginen da aka gina a kan magudanar ruwa.”
“Gwamnatin jihar Legas ta fara kawar da haramtattun gine-gine, gine-gine ba tare da amincewar doka ba a rukunin kasuwanci da ke ƙaramar hukumar Ojo,” inji Gawat.
Har ila yau, akwai ofishin samar da ababen more rayuwa, da ‘yan majalisar dokokin jihar Legas, da jami’an tsaro waɗanda suka bayar da tallafi a lokacin aiwatar da aikin.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Legas, a makon da ya gabata, ta bayar da umarnin dakatar da duk wasu ayyukan sake gine-gine a faɗin jihar nan take, saboda illar muhalli.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Tokunbo Wahab, wanda ya sanar da hakan, ya ce ma’aikatar ta lura da yadda ake samun yawaitar ayyukan gine-gine kan magudanar ruwa a wuraren da suke da dausayi a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da “Parkɓiew, Banana Island, Osborne, Ikoyi, ɓictoria Island Eɗtension, Lekki, Ajah, Oworonshoki, da kuma sassan Ikorodu”.
Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa ayyuka da dama ba su da sahihin amincewar tantance tasirin muhalli da kuma magudanar ruwa daga ma’aikatar.
