Duk ɗaya daga cikin yara shida a Arewacin Nijeriya na mutuwa kafin shekara biyar – Bill Gates

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hamshaƙin attajirin nan na Amurka, Bill Gates, ya yi wani kakkausan gargaɗi game da mummunar mace-macen ƙananan yara a arewacin Nijeriya, inda ɗaya daga cikin yara shida da aka haifa a yankin ba ya rayuwa har ya kai shekaru biyar.

Gates ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi gabanin taron masu tsaron gida na shekara-shekara na gidauniyar Bill & Melinda Gates a birnin New York, inda ya bayyana ƙididdigar a matsayin “kira ta farkawa” ga shugabannin Nijeriya da abokan ci gaba.

“Yaron da aka haifa a arewacin Nijeriya yana da kashi 15 cikin 100 na damar mutuwa kafin ya kai shekaru biyar. Ko dai ku zama wani ɓangare na inganta hakan ko kuma ku yi ƙoƙarin kawar da shi,” inji Gates.

Attajirin nan mai bayar da agajin ya yi nuni da cewa, yayin da aka samu gagarumin ci gaba a duniya wajen rage mace-macen yara, har yanzu Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fama da yawan mace-mace yara saboda raunin tsarin kiwon lafiya, talauci, rashin abinci mai gina jiki, da rashin tsaro.

Don ci gaba da yaƙi da mace-macen yara da za a iya daƙilewa, Gidauniyar Gates ta sanar da yin alƙawarin dala miliyan 912 ga Asusun Duniya don Yaƙar AIDS, tarin fuka, da zazzaɓin cizon sauro na 2026-2028.

Ana sa ran tallafin zai ƙarfafa nasarorin da tuni ya rage mace-macen yara a duniya da rabi tun daga shekara ta 2000 daga mutuwar miliyan 10 a kowace shekara zuwa ƙasa da miliyan biyar.

Sai dai Gates ya yi gargaɗin cewa waɗannan nasarorin ba su da rauni, yana mai lura da cewa kuɗaɗen tallafin kiwon lafiya na ƙasa da ƙasa sun ragu da fiye da kashi 20 cikin 100 a bara, inda ya kai matsayin mafi ƙaranci cikin shekaru 15.

“Ba ni da ikon yin abin da gwamnati za ta yi, kuma ba na so in haifar da ruɗani,” inji Gates, yana mai jaddada cewa ba da agaji ba zai iya maye gurbin alhakin gwamnati ba.

Gates ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta ƙarfafa fannin kiwon lafiya a matakin farko, da faɗaɗa hanyoyin samar da alluran rigakafi da kuma saka hannun jari kan sabbin sabbin hanyoyin kiwon lafiya, inda ya ƙara da cewa, za a iya ceton wasu miliyoyin yara a duniya nan da shekarar 2045 idan shugabanni suka sake dagewa wajen tabbatar da dabarun rayuwa.

By ukarofi