Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta tabbatar da cewa ta samu takardun kotu da ke hana mambobinta sayar da tikiti ko duk wani yunƙuri da zai kawo tsaikon al’amura a Matatar ɗangote.
Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja ranar Talata, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Gas (PENGASSAN).
Akporeha ya ce ƙungiyar tana mutunta doka, kuma za ta bari shari’a ta yi aikinta har sai an kammala duk wani sha’ani a kotu.
“Kamar yadda kowa ya sani, ɗangote ya kai mu kotu, kuma yanzu mun samu umarnin kotu da ya hana mu sayar da tikiti ko datse duk wata hanya zuwa harabar matatarsa. Za mu ci gaba da kiyaye wannan doka, mu bar shari’a ta yi aikinta,” inji shi.
Manhaja ta ruwaito yadda a makon da ya gabata, Kotu Masana’antu da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi da ya hana ƙungiyar shiga yajin aiki ko tilasta wa direbobin manyan motoci rajista da ita.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a E.D. Subilim, ya bayar da wannan umarni, wanda ya shafi ƙungiyar Direbobin Motoci Masu Dakon Man Fetur, inda ya hana su rufe hanyoyin Nijeriya ko daƙile ayyukan Matatar ɗangote, MRS Oil Nigeria Plc, da MRS Oil and Gas Company Ltd.
A yayin taron, NUPENG ta musanta zargin cewa tana karɓar N50,000 daga manyan motocin da ke ɗaukar mai a daffo-daffo.
“Ba NUPENG kaɗai ke aiki a daffo-daffon ba. Akwai wasu ƙungiyoyi da ke aiki a wuraren. Don haka batun cewa NUPENG tana karɓar N50,000 ba gaskiya ba ne,” inji Akporeha.
