Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Kungiyar masu fitar da kaya ƙarƙashin shugabancin shugabanta na Kano, Alhaji Hafizu Lurwanu, ta gudanar da taro na musamman a Kano a ranar Juma’a da ta gabata, inda shugabannin reshen ƙungiyar da dama suka halarta. Wannan ƙungiya ce mai suna Association of Nigerian Licensed Customs Agents (ANLCA), wacce ke da izinin gudanar da harkokin fitar da kaya bisa ƙa’ida da doka.
A jawabinsa, Alhaji Hafizu ya bayyana cewa ƙungiyar na da dimbin mambobi, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce babban manufar wannan taro ita ce jawo hankalin mambobin ƙungiyar kan buƙatar ci gaba da bin doka da ƙa’idoji a harkokinsu, tare da inganta mu’amala da abokan hulɗa.
Ya ƙara da cewa ANLCA na da kyakkyawar fahimta da jami’an Hukumar Hana Fasa-ƙauri ta ƙasa (NCS), kasancewar ƙungiyar ta tsayu kan tafiyar da harkokinta bisa ƙa’ida. Ya kuma shawarci mambobin ƙungiyar da su ci gaba da bin dokoki da ƙa’idoji, musamman kan tattaunawar da ake yi game da ƙarin haraji na kashi huɗu, wanda har yanzu ba a tabbatar da aiwatar da shi ba kamar yadda bayanai ke nuna a halin yanzu.
