Haƙurinku ba zai tafi a banza ba – Tinubu ga ƴan Nijeriya kan salon mulkinsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa al’ummar Nijeriya kan yadda suke jure wa halin matsin rayuwa a ƙasar ta dalilin gyare-gyaren da yake yi wa harkar tattalin arziƙi tun sadda ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Tinubu ya bayyana wahalar da ƴan Nijeriya ke sha a sanadiyyar haka a matsayin raɗaɗin da wanda ake yi wa magani yake ji, yana mai cewa nan gaba za a mori sakamakon gyare-gyaren da gwamnatin nasa ke yi.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne yayin jawabinsa a taron naɗa sarkin Masarautar Ibadan na 44, wato Mai Martaba Oba Rashidi Adewolu Ladoja a ɗakin taro na Mapo da ke Ibadan a jiya Juma’a.

Ya kuma yi wa al’umma albishir da cewa harkar tattalin ta ɗauki salo mai alfanu a gare su da ma ƙasar baki ɗaya, wanda a cewarsa za a samu gagarumar nasara a nan gaba saboda haka.

Ya bayyana cewa, hakan da yake yi abu da ke da matuƙar amfani ga al’umma da ƙasar domin samar da tabbatuwar ɗorewar tattali a ƙasar.

By Babaji