PENGASSAN ta dakatar da kai wa Matatar Ɗangote fetur da gas

Spread the love

Kungiyar Ma’aikatan Albarkatun Man Fetur da Gas ta Manyan Ma’aikata (PENGASSAN) ta ɗauki mataki mai tsauri kan Matatar Man Fetur ta Dangote bayan rikicin ma’aikata ya tsananta.

A ranar Asabar ƙungiyar ta umarci rassanta guda bakwai da su dakatar da isar da man fetur da gas zuwa matatar mai darajar dala biliyan 20 da ke Lekki, Jihar Legas.

A wani saƙo daga sakatarenta, Lumumba Okugbawa, PENGASSAN ta zargi shugabancin matatar da korar mambobinta saboda shiga kungiyar ƙwadago.

Ta ce, wannan mataki na matatar ya saɓa wa ƴancin ma’aikata na shiga kungiya, inda ta kara da cewa ma’aikatan gida an hana su shiga wurin aiki yayin da ake baiwa kwararrun kasashen waje damar shiga.

Ƙungiyar ta kuma ba da umarni kai-tsaye ga shugabannin rassanta a manyan kamfanonin man fetur da gas kamar su TotalEnergies, Chevron, Seplat, Shell Nigeria Gas, Oando da NGIC da su dakatar da duk wata isar da man fetur da gas zuwa matatar Dangote. Ta kuma yi gargadin cewa za ta yi zanga-zanga a gaban matatar idan ba a magance matsalar ba.

Saidai a martanin da ta fitar a ranar Juma’a, matatar Dangote ta musanta zargin korar ma’aikata da yawa, inda ta ce ma’aikata sama da 3,000 na Najeriya har yanzu suna aiki a wurin. Ta bayyana cewa sabon tsarin da ta aiwatar bai nufi tsananta wa ma’aikata ba, sai dai kare rayuka da hana yiwuwar barna a sassa daban-daban na matatar.

PENGASSAN ta bayyana cewa matakin ya zama dole domin nuna adawa da abin da ta kira “take hakkin ma’aikata” tare da kiran shugabannin rassan NGIC da su tabbatar an dakatar da isar da gas nan take.

By Babaji