An sace motar ƴan sanda a hedikwatar rundunar ta ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa wasu ɓata-gari sun yi nasarar sace wata motar aiki ta ofis ƙirar Toyota Buffalo Land Cruiser a harabar hedikwatarta na Louis Edet House a Abuja.

Sashen binciken manyan laifuka na FCID ya tabbatar da haka a wata takarda, ta hannun kwamishinan ƴan sanda na DFA ofishin Katsina.

Ya bayyana cewa motar tana ɗauke ne da lambar rijista kamar haka: NPF 5594 D da casis mai lamba JTELU71JX0B027126, wadda ta ɓace tun a ranar 28 ga Yuli, 2025 daga wurin ajiye motoci na hedikwatar.

Jami’in ua ƙara da cewa, motar ta kasance a ƙarƙashin Sashen Ayyuka, wato Department of Operations na rundunar. An gano ɓacewarta ne bayan gano cewa an cire ta daga inda aka ajiye ta.

A cikin sakon da rundunar ta fitar, an ce: “An sanar da mu cewa motar runduna mai lambar rijista NPF 5594 D da aka ɗora wa Sashen Ayyuka na Hedikwatar Abuja an bayyana cewa an sace ta ko kuma an cire ta daga wurin ajiye motoci a ranar 28/07/2025. Ana ci gaba da bincike dai. Dukkanin kwamandoji, DPOs da sauran rukuni na rundunar a fadin ƙasa su sanya ido domin gano motar.”

Hukumar ta buƙaci dukkan jami’an tsaro a faɗin Nijeriya da su ɗauki lamarin da matuƙar muhimmanci, tare da ba da rahoto nan take idan aka samu wani sahihin bayani da zai taimaka wa aikin gano ta

.

By Babaji