
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba, 1 ga watan Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutu domin karrama cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ƴancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana haka a madadin gwamnatin tarayya inda ya kuma ya taya ɗaukacin al’ummar ƙasa murna.
Ya yi kira ga al’umma da su cigaba da kasancewa masu kishin ƙasa da haɗin kai a tsakaninsu waɗanda hakan suka sa ƙasar ta ke samun nasarori tun ba ta ƴanci a 1960.
Haka kuma, Tunji-Ojo ya kirayi ƴan ƙasa da su cigaba da sa tsammani akan shirin sabunta fata na Shugaba Bola Tinubu, wanda an gina shi ne akan sake gina ƙasa, inganta tattalin arziƙi da nasarori daga kowane ɓangaren ƙasar.
A ƙarshe, ya yi wa al’umma barka da murnar ranar ƴancin kai ta 2025 da fatan a kammala lafiya, kamar yadda sanarwar da Sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar ya bayyana.
