Jawabin ranar ƴancin kai: Tinubu ya jinjina wa ƴan mazan jiya da lissafo nasarorin da gwamnatinsa ta samu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yayin jawabinsa na ƙasa a safiyar yau Laraba da Nijeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai, Shugaba Bola Tinubu ya yi jinjina ga ƴan mazan jiya da kuma zayyano wasu nasarori da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Tinubu, wanda wannan shi ne karo na uku da yake gabatar da jawabin ƴancin kai a matsayin shugaban ƙasa, ya ce wannan lokaci ne na nazarin muhimman al’amuran ƙasa da sabunta fata.

Ya yaba wa sadaukarwar da ƴan mazan jiya suka yi wa ƙasar kamar su Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo, Ahmadu Bello, Tafawa Ɓalewa, Margaret Ekpo, da Funmilayo Ransome-Kuti.

Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci akan ƙalubale da yaƙe-yaƙen da suka addabi sassan ƙasar waɗanda suak haɗa da yaƙin basasa, juyin mulkin, mulkin kama karya, ta’addanci da taɓarɓarewar tattalin arziƙi, wadda ƙasar ta iya jurewa akansu.

Ya tunatar da cewa Nijeriya a shekarar 1960 tana da manyan makarantu biyu ne kaɗai – Jami’ar Ibadan da kuma Kwalejin Fasaha ta Yaba, inda a yanzu kuma take da jami’o’i aƙalla guda 274, polytechnics 183 da kwalejin ilimi 236.

Daga nan sai ya lissafo nasarori guda 12 da kaa samu a ƙarƙashin mulkinsa waɗanda dafa ciki akwai:
Tara Naira tiriliyan 20 na kuɗin haraji (banda na mai) zuwa Agustan 2025, wanda hakan ya kere abinda aka hara.
Kuɗin ajiya a waje da haura zuwa Dala biliyan 42.03, wanda shi ne mafi yawa tun a 2019.
Adadin kuɗin biyan bashi daga kuɗaɗen haraji ya ragu daga kaso 97 zuwa 50.
Kuɗin shiga da kayayyakin da ake samarwa ya hauhawa zuwa kaso 4.23.
Hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kaso 20.12, wanda shi mafi sauka a shekarar uku.
Haɓakar kasuwanci ya kai darajar Naira tiriliyan 7.46, yayin da kayayyakin da ake shigowa da su (banda mai) suka haura zuwa kaso 48.
Samar da mai ya haura zuwa ganga 1.68 a kullum, yayin da matatun gida suka koma aiki bayan shekaru 40.
An raba tallafin kuɗaɗe ga magidanta miliyan 8 da adadinsu ya kai biliyan N330.
Sai ayyuka layin dogo, tituna filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa, aikin babban titin Legas zuwa Kalaba da kuma aikin layin dogo na gabas da ke tafe.

Kazalika, yi murna da farfaɗo da janyo ra’ayoyin masu zuba jari daga ƙasashen waje a harkokin kasuwanci da wasu kamfanonin gwamnati.

Game da lamarin tsaro kuwa, Tinubu ya ce a yaƙin da dakarun tsaron Nijeriya ke yi wajen daƙile ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka, an samu zaman lafiya a ɗaruruwan garuruwa a yankunan Arewa ta Gabas da ta Yamma.

Sauran batutuwan da gwamnatin nasa ta yi nasarar akan su sun haɗa da inganta matasa musamman ɗalibai ta shirin NELFUND, wanda a cewarsa aƙalla mutane 510,000 ne suka amfana da tallafin kuɗaɗe na ‘YouthCred and Cedicorp’, shirin iDICE da dai sauransu, yana mai kira ga ƴan Nijeriya da su cigaba da ba gwamnatinsa goyon baya wajen gyare-gyarenta domin ciyar da ƙasar gaba.

By Babaji