
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sarkin Masarautar Ibadan na 44, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, wato Arusa na I, ya sanar da yin murabus daga harkokin siyasa bayan rantsar da shi a matsayin sarki.
Sarkin, wanda tsohon gwamnan Jihar Oyo ne, ya faɗi haka ne a jiya Talata yayin da ya karɓi baƙoncin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Iyorchia Ayu da wasu masu alfarma a Fadarsa da ke Ibadan.
Oba Ladoja ya ce, ya yanke hukuncin ne saboda sabon muƙamin da ya samu na zama sarkin.
Ya kuma tuno da zangonsa na siyasa tare da su Atiku da wasu musamman a lokacin da suke cikin jam’iyyun SDP da PDP, inda daga bisani suka samar da ‘Accord Party’, wato AP.
“Ni yanzu ba ɗaya daga cikin ku ba ne. Ni ba ɗan siyasa ba ne yanzu. Yanzu da nake sarkin Masarautar Ibadan, ba na ra’ayin komai in ba sarautar ba. Ina muku maraba da zuwa gidana”, inji Sarkin.
Ya kuma ce, zangonsa na sarautar zai kasance mai adalci da ƙoƙarin tabbatar da gaskiya bisa la’akari da shawarwarin jagororin addini.
