Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban Ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya Abdullahi, ya yi kira ga ’yan jarida su rungumi aikin jarida a matsayin mafita ko hanyar shawo kan matsalolin da ke addabar Arewacin Najeriya.
Dr Al Hassan ya yi wannan kira ne a wajen taron cika shekara 38 da ƙirƙiro, jihar Katsina wanda aka gudanar a Hayatt Regency Suite bisa jagorancin ƙungiyar NUJ ta Jihar Katsina.
Abdullahi ya bayyana damuwa kan matsalolin ilimi, kiwon lafiya, da talauci da ke ƙara taɓarɓarewa a jihohin Arewa, inda ya ambaci yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, matsalar rashin abinci mai gina jiki, rashin wadatattun asibitoci, da kuma tsaro a matsayin manyan ƙalubale.
“Tun sama da shekaru 25 da suka gabata, alamun gargaɗi sun bayyana. Arewacin Najeriya ta faɗi a ɓangaren ilimi, lafiya da kuma talauci. “Ya kamata mu ɗauki matakin saita ajandar da za ta kawo sauyi mai ma’ana,” in ji shi.
Shugaban na NUJ ya jaddada nauyin da ya rataya a wuyan ’yan jarida wajen ba wa marasa galihu murya da kuma riƙe shugabanni da alhakin aikinsu, yana mai cewa rahotannin da ke kawo mafita na iya share fagen zaman lafiya da ci gaba.
Ya kuma yi kira kan muhimmancin ba da horo da koyi daga dattawan ’yan jarida ga matasa da ke tasowa, yana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci ga makomar sana’ar.
Dangane da jin daɗin ma’aikata, Abdullahi ya bayyana cewa NUJ na shirin fito da sabon tsarin albashi da kuma tabbatar da inshora ga ’yan jarida, musamman waɗanda ke aiki a yankunan da rikici ya fi shafa.
“Bincike ya nuna cewa ƙasa da kashi ɗaya cikin ɗari na ’yan jarida a Najeriya ke da inshora. Wannan dole ya sauya. A ƙarƙashin jagorancina, NUJ za ta yi aiki tuƙuru don ganin an samar da kariya da kuma ingantaccen sakamako ga ’yan jarida,” in ji shi.
Shugaban ƙungiyar ya yaba wa gwamnatin jihar Katsina bisa haɗin kai da ƙungiyar NUJ tare da kiran ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ’yan jarida da masu tsara manufofi wajen inganta makomar Arewacin Najeriya.
Ya kammala da nuna kyakkyawan fata cewa, ta hanyar haɗin gwiwa da kuma ƴan jaridu a matsayin mafita, hakan zai sa Arewacin Najeriya su iya shawo kan manyan ƙalubalen da suka daɗe suna fama da su.
