Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An naɗa Kwamred Muhammad Musa Inyya, tsohon Mataimakin Darakta a gidan rediyon Kano FM, kuma tsohon shugaban ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin da Wasan Kwaikwayo ta ƙasa (NARTO) reshen Kano, a matsayin sabon Shugaban Gidan Rediyo da Talabijin na Hikima Rediyo.
Naɗin ya biyo bayan sanarwar da Hon. Ibrahim Sha’aban Sharaɗa, mamallakin Hikima Rediyo kuma Shugaban Hukumar Zartarwa ta gidan rediyon ya fitar a tsakiyar makon da ya gabata. Sanarwar ta tabbatar da cewa Malam Inyya ya fara aiki a muƙaminsa tun ranar Laraba.
A cewar Hon. Sha’aban Sharaɗa, tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kano Municipal da tsohon shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, Malam Inyya ya cancanci wannan muƙami bisa gogewa, jajircewa, da kyakkyawar mu’amala da abokan aiki da al’umma.
Tuni ‘yan uwa da abokan aiki suka yi ta taya shi murna da addu’ar Allah ya masa jagora wajen gudanar da aikin da zai kawo cigaba ga al’ummar Kano da Nijeriya baki ɗaya, bisa hazaƙa, hangen nesa da ƙwarewar da Allah ya yi masa.
