Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Daya daga cikin jagororin Sharifan Nijeriya, Alhaji Sharif Haruna Abba Garinali, ya bayyana cewa adawar da ƙungiyar Izala ta yi kan ɗariƙun sufaye ta ƙara bunƙasa su maimakon rage tasirinsu.
Ya ce kafin wannan adawa, wasu daga cikin mabiya tariƙa ba sa tsayawa da ƙarfi wajen bin hanyarsu, amma bayan adawar, sai suka ƙara zurfafa ilimi da bincike tare da riƙe aƙidarsu da ƙarfi. Ya ƙara da cewa zuwan Izala ya ƙara haɓaka tarurrukan Maulidi, wanda yanzu suka fi yawa da bunƙasa fiye da da.
Sharif Haruna ya jaddada cewa a tarihin Musulunci akwai irin wannan ƙiyayya da ta kai ga Manzon Allah yin hijira, don haka adalci shi ne mafita ga kowanne irin sabani.
Ya yi kira da cewa masu tafarki su rungumi godiya ga Allah, su kauce wa neman suna da tasiri da sunan addini, su mai da hankali wajen wa’azi da musuluntar da waɗanda ba musulmi ba. Ya kuma gargaɗi jama’a da su guji faɗar abin da ba zai amfanar da addini ba, domin gaskiya a bayyane take.
