Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ranar Talata ne shari’ar tsohon gwamnan Jihar Taraba, Architect Darius Ishaku, da tsohon babban sakatare, Alhaji Bello Yero, ta ɗauki sabon salo a babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama, inda shaidar masu gabatar da ƙara na farko ya amince cewa bai san adadin kuɗaɗen da ake zargin ya karɓa a madadin tsohon gwamnan ba.
Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) na gurfanar da Ishaku da Yero a gaban Mai Shari’a Sylɓanus Oriji kan tuhume-tuhume 15 masu lamba FCT/HC/CR/792/2024. Laifukan sun ci karo da laifukan da suka shafi cin amana, haɗa baki, da musayar kuɗaɗen jama’a da suka kai Naira Biliyan 27. Duk da haka, duk waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Shaidan mai gabatar da ƙara na farko, Ismail Oluwadamilare Lawal, wanda ya kasance mataimaki na musamman ga Ishaku, ya shaida wa kotun a lokacin da lauyan da ke kare wanda ake tuhuma Paul Ogbole, SAN ya yi masa tambayoyi, cewa yayin da yake karɓar alawus-alawus ɗin da ya samu a madadin tsohon gwamnan, bai san takamammen kuɗaɗen da aka samu ba ko kuma ranar da ya karɓa.
“Na tattara alawus-alawus ɗin wanda ake ƙara na farko na raba su bisa ga umarninsa. Amma ban san adadin da na karɓa a madadinsa ba, kuma ban san kwanan watan ba,” inji Lawal.
Lawal ya ƙara da cewa shi ma yana karɓar alawus-alawus na hidima da suka haɗa da N20,000 a kullum yayin tafiya tare da gwamnan, baya ga albashin da yake karɓa na N130,000 duk wata.
Ya kuma bayyana cewa, ya yi sana’ar kiwon kaji a Kubwa, Abuja, tare da tsuntsaye kimanin 6,000 a lokacin, wanda daga baya ya ragu zuwa 2,000, wanda darajarsa ta kai kimanin naira miliyan biyar.
Tun da farko dai mai gabatar da aara ya gabatar da wani littafi da Lawal ya ajiye a matsayin shaida. Da aka yi masa tambayoyi, shaidan ya yarda cewa abubuwan da aka rubuta a cikin littafin ba na gwamnati ba ne ko na banki kuma jami’an da suka ba shi kuɗi ba su sa hannu ba. Ya ƙara da cewa bayanan sirri ne, wanda aka ajiye tsakaninsa da gwamnan.
Ya kuma bayyana cewa Ishaku ne ya umarce shi da ya tafi Legas, inda ya kwana a otel a kan Naira 20,000 a kowane dare, inda ya kai kusan N600,000 a kowane wata a tsawon shekara ɗaya da wata bakwai.
Sai dai ya ce, bai bayar da takardar shaidar ko daya ba, domin jami’an EFCC sun kwace wasu takardunsa a lokacin da aka kama shi a Legas.
Lawal ya tabbatar da cewa bayan kama shi, an kai shi ofishin EFCC na Legas kafin daga bisani a wuce da shi Abuja, inda ya yi bayani ga masu bincike.
