
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban hukumar zaɓe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga muƙaminsa tare da miƙa ragamar jagorancin hukumar ga May Agbamuche-Mbu, wadda za ta riƙe muƙamin a matsayin riko kafin naɗa sabon shugaba.
Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne yau Talata yayin ganawa da kwamishinonin hukumar a hedikwatarta da ke Abuja.
Agbamuche ita ce wadda ta fi kowa jimawa a matsayin babbar kwamishina a INEC.
Ya kuma kirayi sauran kwamishinoni da daraktocin hukumar da su bai wa Agbamuche-Mbu cikakken goyon bayan kafin lokacin naɗa sabon shugaban hukumar.
A watan Oktoban 2015 tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi, Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.
Haka kuma ya sake naɗa shi a muƙamin a shekarar 2020 domin cigaba da jagorantar hukumar a karo na biyu.
Farfesa Yakubu ya jagoranci hukumar har na tsawon shekaru 10, inda ja ragamar gudanar da manyan zaɓukan ƙasar a 2019 da 2023.
