ADC ta fara aikin yi wa jam’iyyar kwaskwarima

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar African Democratic Party, ADC, ta amince da kundin tsarin mulkin kwamitocinta na sake suna da sake duba kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron ƙaddamar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC) a ranar Talata a Abuja.

Mista Abdullahi ya ce kwamitin NWC ya kuma amince da kundin tsarin mulki na shawarwarin manufofi da kwamitocin rijistar membobinsu.

“Kwamitin ayyukan NWC ya kuma amince da ranakun da za a gudanar da zaɓukan fidda gwani na Ekiti da Osun. Za a gudanar da zaɓen fidda gwani na Ekiti daga ranar 10 ga watan Oktoba zuwa 20 ga Nuwamba. Osun zai gudana tsakanin Nuwamba da Disamba,” inji shi.

Mista Abdullahi ya ci gaba da cewa, duba da yadda da yawa daga cikin jihohin ke da shugabanni kawai, kwamitin NWC zai samar da ƙa’idojin tafiyar da harkokin jam’iyyar kafin babban taron da za a yi.

By ukarofi