Tinubu ya taya Namadi Sambo murnar zama Sardaunan Zazzau

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Namadi Sambo murna bayan da Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya naɗa shi a matsayin Sardaunan Zazzau.

A makon da ya gabata ne aka gudanar da naɗin a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

A wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya ce muƙamin abu ne da ke da matuƙar daraja a al’adu da tarihi na Arewacin Nijeriya.

Haka kuma ya nuna yadda Masarautar Zazzau ta amince da basira, gaskiya da jajircewar Namadi Sambo wajen ci-gaban al’umma.

Shugaban ya ce, wannan girmamawa alama ce ta jagoranci nagari da gudummawar Sambo ga ci-gaban ƙasa tun daga lokacin da ya riƙe manyan muƙamai a gwamnati.

Ya kuma yaba wa Sarkin Zazzau bisa ci gaba da riƙe al’adar girmama mutanen da suka yi fice wajen jagoranci, kishin ƙasa da kuma ɗorewar zaman lafiya.

Shugaba Tinubu ya yi fatan Allah ya ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa nasara a sabuwar rawar da zai taka, tare da kira gare shi da ya ci gaba da zama abin koyi ga matasa da kuma yin aiki kafada da kafada da shugabannin gargajiya domin ci gaban al’umma da ƙasar baki ɗaya.

By Babaji