
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano za ta raba katan 155 na gyaɗar tamowa ga ƙananan yara da suke fama da cutar tamowa a yankin.
Kansilan Sashen Lafiya na Ƙaramar Hukumar, Malam Bashir Sabi’u Magaji Saye ne ya faɗi haka yayin ƙaddamar da shirin bada tallafin, a sakatariyar Ƙaramar Hukumar.
A wata takarda da Jami’ar Yaɗa Labarai ta Karamar Hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce jami’in ya ce zai cigaba da ƙoƙarin gudanar da aiki a kowane fanni, musamman ɓangaren lafiya karkashin jagorancin Ciyaman ɗin Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata.
Ƙaramar hukumar ta bayyana wasu asibitoci da iyayen yara masu fama da larurar tamowa a yankin za su cigaba da karɓar madarar ta tamowa da suka haɗa da; asibitocin Saye, Ɗan-Zabuwa, Badume, Dutsen-Karya da kuma Malikawa-Garu.
Da yake jawabi Shugaban Sashen Lafiya na Ƙaramar Hukumar, Malam Kabiru Abubakar Gwarzo, ya bayyana cewa za a samar da katan 31 na madarar tamowa a asibitocin domin gajiyar yara masu fama da matsalar tamowa.
“Kowane yaro zai samu katan daya, saboda sai ya gama sha gaba daya domin kada ta yanke; shi ya sa ake ware musu, da nufin in Allah ya yarda kafin ta kare yaro zai warke daga wannan cuta ta tamowa. Don haka adadin yara masu larurar da za su amfana a kowane asibiti su 31”, inji shi.
Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya ja hankalin jami’an lafiya da aka ɗora wa alhakin raba gyadar tamowar da su ji tsoron Allah su tsaftace aikinsu, kuma su guji ha’inci wajen gudanar da aikin.
Bisa haka, ya dauki mutum biyu a kowace mazaɓar da za su saka ido yayin aiwatar da aikin domin kiyaye dukiyar al’umma da kuma tabbatar da adalci a tsakaninsu.





