
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025 Kwalejin Koyon Yaƙi ta Sojoji (AWCN) ta gudanar da bikin ƙarin matsayi ga wasu jami’ai 14 ƴan rukuni na 9/2025.
An gudanar da taron ne a babban ɗakin taro na kwalejin mai suna Tukur Yusuf Buratai Auditorium a Asokoro da ke Birnin Tarayya Abuja.
Da yake jagorantar taron, Kwamandan AWCN, Manjo Janar Umar Mohammed Alƙali, ya yaba wa jami’an kan samun ƙarin matsayin bisa cancanta, yana mai bayyana haka a matsayin kira ga ƙara zage damtse wajen hidimta wa ƙasa.
Ya kiraye su da su kasance masu mayar da hankali, horo da ƙirƙira wajen magance matsalolin ƙalubalen tsaro a zamanance.
Ya bayyana cewa, ƙarin matsayi a rundunar soja abu ne da ke nufin sa rai da samun gagarumar hidima musamman daga jami’ai a matakin gudanarwa, don haka su kasance abin koyi ga ƴan baya da kuma ƙoƙarin kare martabar rundunar soji a Nijeriya.
Kazalika, Manjo Janar Alƙali ya buƙace su da su riƙa fifita walwalar dakarunsu da iyalansu ba tare da la’akari da inda aka tura su aiki ko wurin da suka ƙware ba.
Sababbin waɗanda aka ƙara matsayin sun haɗa da; “Lt Col AE Oladipo, Lt Col DB Fapohunda, Lt Col UB Mai Garba, Lt Col LA Adejo, Lt Col EA Kaan, Lt Col M Mohammed, Lt Col YI Isiaku, Lt Col ZA Sadau, Lt Col SA Arogundade, Lt Col AO Ochigo, Lt Col MD Adamu, Lt Col AA Uma, Lt Col DO Ehicheoya, da kuma Lt Col AS Adisa”, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, Manjo Hashimu Sa’ad Abdullahi ya ruwaito.








