Ƙungiyar HURIWA ta caccaki Tinubu kan naɗa Amupitan a matsayin shugaban INEC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar kare ci-gaban ƴancin al’umma ta ƙasa (HURIWA), ta yi tir da naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin shugaban Hukumar Zaɓe (INEC) da Shugaba Bola Tinubu ya yi a makon da ya gabata.

Ta bayyana hakan a matsayin yunƙurin maguɗi a baban zaɓen 2027 wajen bai wa Jam’iyya mai mulki ta APC nasara.

A wata tarda da Shugabanta, Kwamared Emmanuel Onwubiko ya fitar, HURIWA ta zargi Tinubu da naɗa yaronsa domin sanya ido akan lamuran shirye-shiryen zaɓen ƙasar yayin da ake cigaba da tunkarar 2027, tana mai cewa hakan na nuna yadda Tinubu ke son yin ta-zarce ko ta wace hanya.

A cewar ƙungiyar, wani rahoton sirri ya bayyana cewa shugaban ƙasar ya ɗauko ɗan ƙabilarsa ta Yarabawa, wato Farfesan mai shekaru 58 daga Jihar Kogi domin karkatar da hankali akan abinda Tinubu da APC suke son cimmawa a manufarsu ta siyasa musamman a zaɓen 2027.

Kwamared Onwubiko ya ce, rahoton ya kuma nuna cewa an yi naɗin ne ba bisa ƙwarewar da Farfesan yake da ita ba, saidai don a riƙa juya shi yadda ake so, lamarin da ya sa “shugaban ƙasar ya zaɓe shi saboda kusancin alaƙarsu”.

Akan haka ne ƙungiyar ta gargaɗi al’ummar ƙasa da cewa kada su yi tsammanin ganin zaɓe mai cike da gaskiya da adalci a 2027 matuƙar ba a yi wa dokar zaɓe kwaskwarima ba ta yadda za a wajabta yin amfani da na’urorin zamani a zaɓuka kamar na tsarin tantancewa ta BVAS da shafin bayyana sakamakon INEC na IReV.

By Babaji