DAGA JOHN D. WADA, a Lafia
A cewar kwamitin lambar yabon na musamman na jaridar Independent Newspaper a wajen taron an bai wa Gwamna Sule wannan lambar yabo ne saboda gagarumin aikinsa a fannin ilimi ta hanyar zuba jari da wayar da kawuna da kuma tallafa wa ilimin yara a jihar sa ta Nasarawa dama ƙasa baki ɗaya.
Wata sanarwa daga babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Ibrahim Addra daga bisani da aka raba wa manema labarai ciki har da wakilin mu ya bayyana cewa wannan karramawar ta kuma nuna yadda gwamna Sule ke ƙoƙari wajen faɗaɗa damar samun ilimi, inganta koyarwa da kuma ƙarfafa koyon sana’o’in da ke da amfani a rayuwar al’umma a faɗin jihar.
Gwamna Sule ya samu wakilcin kwamishinan Ilimin jihar Dr. John D. W. Mamman a yayin taron wadda yazo dai dai da bikin cika shekaru 70 da ƙaddamar da ilimin kyauta a Najeriya wato Free Basic Education in Nigeria a turance wadda aka gudanar a ranar Alhamis na makon jiya a Legas.
A cikin jawabin sa wanda ya wakilci gwamna Sule wato Dokta John W. Mamman ya gode wa shugabancin jaridar Independent Newspaper saboda hangen nesa da jajircewar Gwamna Sule da suka yi wajen inganta ci gaban ɗan Adam ta hanyar ilimi.
Gwamnan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da bai wa ilimi muhimmanci, kasancewar sa muhimmin abin da ke haifar da ci gaba da ƙarfafa al’umma.
Bikin ya samu halartar fitattun ’yan Najeriya, ciki har da babban dattijo Cif Bisi Akande wanda shi ne shugaban taron da Farfesa Uche Azikiwe wato matar marigayi Dr. Nnamdi Azikiwe da tsoffin ministoci da Farfesa Barth Nnaji da Otunba Olusegun Runsewe da Alhaji Lai Mohammed da jikokin marigayi Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello da fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen nan Dokta Danladi Bako da kuma sakatariyar zartarwa ta hukumar UBEC dakta Aisha Garba da sauran manyan baƙi.
