Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan takarar Ƙaura Namoda ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Muhammad Lawal Kurya ya bar jam’iyyar sa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a ƙasa.
Zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ranar 16 ga watan Satumba, 2025 inda APC ta yi nasara da gagarumin rinjaye inda ta doke jam’iyyar PDP mai mulki, Muhammad Lawal Kurya shine ya tsaya takarar a Ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Muhammad Lawal Kurya ya bayyana goyon bayan sa ga jam’iyyar APC a wajen wani taro da ƙungiyar Hon. Yazid Shehu Danfulani Project ta shirya, wanda ya gudana a Taula Event Center Gusau yau Asabar.
Muhammad Lawal Kurya ya ce rashin alƙiblar da ke tattare da tsohuwar jam’iyyar sa ta PDP ne ya sanya ya fice daga PDP.
Ya kuma yi nuni da cewa ya fahimci cewa a lokacin zaɓen cike gurbin, sama da kashi 90 cikin 100 na masu zaɓe musamman matasa magoya bayan jam’iyyar APC ne duk da cewa PDP ke mulki a jihar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa zaiyi ƙoƙari tare da magoya bayan sa don ci gaba da samun nasarar jam’iyyar APC a jihar.
Da yake karɓar Muhammad Lawal Kurya da magoya bayan sa, sakataren yaɗa labarai na APC na jihar, Yusuf Idris Gusau ya bayyana farin cikinsa kan wannan cigaba da aka samu tare da tabbatar da cewa APC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da za ta ci zaɓe a Jihar Zamfara.
Sakataren yaɗa labaran ya sanar da su cewa jam’iyyar APC za ta tafi dasu daidai da sauran ‘ya’yan jam’iyyar ba tare da nuna banbanci ba.
Ya kuma buƙace su da su ci gaba da zama ‘yan ƙasa nagari da bin doka da oda don samun nasarar jam’iyyar a jihar.
Yusuf Idris, ya gode wa shugabannin jam’iyyar na jihar musamman tsofaffin gwamnoni Bello Mohammed Matawalle a yanzu ƙaramin ministan tsaro da kuma Abdulaziz Yari Abubakar a yanzu Sanatan Tarayyar Najeriya bisa kyakkyawan jagorancin su ga jam’iyyar.
Ya bayyana cewa APC na da ƙwarin gwiwar sake ƙwato Zamfara a 2027 duba da farin jinin ta da haɗin kan jam’iyyar a jihar.
Yusuf Idris ya ci gaba da cewa da yawa daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP a faɗin jihar Zamfara ba da jimawa ba za su koma jam’iyyar APC domin tuni aka kammala shirye-shiryen gudanar da amsar su.
