Tsarin cinikin ɗanyen mai da Naira zai ci gaba da aiki – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiwatar da tsarin “ɗanyen mai a naira” da ake amfani da shi wajen tallafa wa masu tace mai na cikin gida, domin rage kuɗin tace mai da canjin farashin dalar Amurka.

ƙaramin Ministan Albarkatun Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya bayyana haka a taron ƙungiyar Masu Tace Mai ta Nijeriya (CORAN) Summit 2025 da aka gudanar a Legas ranar Talata.

Lokpobiri ya ce, manufar gwamnati ita ce tabbatar da cewa duk ganga ɗaya na mai da ake fitarwa daga Nijeriya na taimakawa wajen biyan buƙatun cikin gida da na ƙasashen waje.

“A matsayin muhimmin ɓangare na tsarin gwamnati, tsarin ‘ɗanyen mai a naira’ zai ci gaba da zama hanya ta rage kuɗin tace mai, kare kamfanoni daga tasirin hauhawar farashin dala, da kuma ƙarfafa masana’antar tace mai ta cikin gida,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da wadatar man ƙasa ga masu tacewa ta hanyar aiwatar da manufar bayar da man ƙasa ga cikin gida (DSCO), yana mai cewa, “Ba wata ƙasa da za ta iya cewa tana da ‘yancin makamashi idan ba ta iya tace nata mai ba.”

Lokpobiri ya bayyana cewa tace mai a gida na da muhimmanci wajen samar da ‘yancin makamashi, ƙirƙirar ayyukan yi, da farfaɗo da masana’antu a ƙasar.

“Mun ga nasarorin kamfanonin cikin gida kamar Dangote Refinery, Waltersmith Petroman, da Aradel Holdings, waɗanda suka nuna cewa ‘yan Nijeriya na da ƙwarewa da ƙarfin gwiwar tace man ƙasarsu,” inji shi.

Ya ce, gwamnati tana da niyyar kafa irin waɗannan matatun mai a duk jihohin da ake hakar mai, domin ƙarfafa tattalin arziki da rage dogaro da shigo da man waje.

Ministan ya kuma tabbatar da cewa an sauƙaƙa tsarin lasisi ta hannun Hukumar Kula da Harkokin Tace Mai (NMDPRA), domin ba da damar zuba jari cikin sauƙi ba tare da cikas na takardu ba.

Lokpobiri ya bayyana cewa gwamnati ta ƙaddamar da West African Fuel Reference Market, wanda zai baiwa Nijeriya damar zama cibiyar tace mai da samar da man da aka tace ga ƙasashen yammacin Afirka.

Ya ce, wannan tsari yana daidaita da burin Tarayyar Afirka (AU) na haɗin gwiwar makamashi da cinikayya a ƙarƙashin yarjejeniyar AFCFTA.

Lokpobiri ya ƙara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa masu tace mai na cikin gida, ta hanyar ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, samar da yanayin kasuwanci mai ɗorewa, da kare hanyoyin isar da man ƙasa daga masu sata da lalata bututun mai.

“Za mu tabbatar da wadatar man ƙasa ga duk masu lasisin tacewa, da ƙara fa’idodi na haraji don jawo sabbin masu zuba jari, da kuma inganta haɗin kai tsakanin Ma’aikatar Mai, NMDPRA, NUPRC da hukumomin tsaro,” inji Lokpobiri.

By ukarofi