Babu shirin sauya Ministan Kuɗi kan rashin lafiyarsa, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Fadar Shugaban Kasa ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa ana shirin maye gurbin Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mr. Wale Edun, wanda yake rashin lafiya a halin yanzu.

Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi karin haske akan hakan a daren Lahadi yayin da jita-jitar ta ci gaba da yaduwa a tsakanin al’umma.

Wannan bayanin na zuwa ne bayan jita-jitar da ta yadu cewa ministan yana cikin matsanancin rashin lafiya kuma har ma an tafi da shi Asibiti a ƙasar waje.

Onanuga ya nanata cewa Yana rashin lafiya ne kawai, sai ya roki jama’a da su yi watsi da jita-jitar ƙarya.

By Babaji