
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunan Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) domin tabbatar da shi a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe (INEC).
Tinubu, a wani saƙo da ya aika wa majalisar zuwa ga shugabanta Godswill Akpabio, ya nemi ta yi nazari a kai da kuma tabbatarwa.
Tuni Akpabio ya miƙa wa kwamitin baki ɗaya ayyukan majalisar don fara aiki akan al’amarin.
A wani ɓangare kuma, Tinubu ya nemi majalisar da ta tabbatar da Misis Ayo Omidiran a matsayin sabuwar shugabar hukumar kula da tabbatar da adalci wajen raba muƙaman gwamnati da arziƙin ƙasa (FCC) da wasu mutane 28 a muƙamin kwamishinonin tarayya.
