WATA SABUWA: Mahaifin Marigayi Bello ya barranta da danginsa, ya yaba wa Tinubu kan yafe wa Maryam Sanda

Spread the love

​Mahaifin Marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmed Bello Isa, ya yaba da afuwar Maryam Sanda daga Shugaba Tinubu​.

Mahaifin marigayin, wanda matarsa, Maryam Sanda, ta kashe a shekarar 2017, ya yaba da afuwar shugaban ƙasa akan surukar tasa.

​A cewarsa, ya daɗe yana yin kokari a boye domin ganin an saki Maryam, wadda aka yanke mata hukuncin kisa tun bayan da aka same ta da laifin kashe mijinta.

​Alhaji Ahmed Bello Isa, wanda ya bayyana wannan a wata tattaunawa ta hadin gwiwa da aka yi a ranar Talata a Abuja tare da Alhaji Garba Sanda, mahaifin Maryam, ya bayyana cewa dalilinsa na yin hakan tausayi ne kawai, kuma yana son a saki surukarsa domin ta kula da ‘ya’yanta biyu da suke kanana, kuma kashe ta ba zai dawo masa da dansa ba.

​Ya bayyana cewa, “a matsayina na Musulmi mai bin addini, na dade da amincewa da abin takaicin da ya faru wanda ya zama abin tattaunawa a bainar jama’a, inda na zabi yin afuwa da barin hukunci ga Allah.”

​“Babu abin da ya fi ciwo kamar mutum ya rasa dansa ta hanyar da na rasa dana, Bilyaminu.

Sai dai, abin da ke ba ni kwanciyar hankali shi ne ya bar ‘ya’ya biyu kyawawa a baya, jikata, Sa’adatu Bilyaminu, da jikana, Bilyaminu Bilyaminu, wanda aka sa wa suna kamar mahaifinsa.

​“Na yafe wa Maryam wadda aka samu da laifin kashe dana. Kafin karshen shari’ar, na yi dukkan kokari don sanar da ‘Yan Sanda da Kotu cewa ban so a gurfanar da ita ba, saboda ban so a ce jikokina, wadanda suka rasa mahaifinsu a cikin yanayi mai ban tausayi, su ma su rasa mahaifiyarsu.

​Abin da ya faru da dana, kuma ban zargi Maryam a kai ba. Sai dai, yanzu da aka yanke mata hukuncin kisa, ina roko da sunan Allah Madaukakin Sarki a yi mata rahama. Idan aka kashe ta, wa zai kula da ‘ya’yanta biyu? Za su taso a matsayin marayu, ba tare da uba ko soyayyar uwa ba,” in ji shi.

​Da aka tambaye shi game da sanarwar da iyalan suka bayar inda suka nuna damuwa game da afuwar Shugaban kasa, sai ya ce “Kowa yana da ‘yancin fadi a cikin iyalinsa amma a matsayina na mahaifin da ya haifa, na yafe mata.

​Shi ma da yake magana, Alhaji Garba Sanda, mahaifin Maryam, ya nuna godiyarsa ta musamman ga Alhaji Bello da dukkan iyalinsa saboda tausayin da suka nuna, inda ya bayyana hakan a matsayin hakikanin nuna imani da gafara.

By Babaji