Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Al’ummar garin Dutsi da kewaye sun karrama Shugaban ƙaramar hukumar Dutsi, Hon Abdulrazak Adamu Kayawa, da kyautar katon Rago da kuma Alƙur’ani mai tsarki, a matsayin yabo da godiya bisa irin ayyukan alheri da ci gaba da yake gudanarwa a yankin.
Taron karramawar ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Hakimin Dutsi, tare da Dattijo Alhaji Jabiru Ibrahim Dutsi, inda manyan mutane, malamai, matasa da sauran masu ruwa da tsaki daga yankin suka halarta.
A cewar wasu daga cikin al’ummar yankin, Hon. Abdulrazak Adamu Kayawa ya gudanar da muhimman ayyuka da suka hada da, gina fanfuna da magudanan ruwa, gyaran maƙabarta, kakkafa fitilu masu amfani da hasken rana (solar streetlights), Da kuma inganta sakateriyar ƙaramar hukumar Dutsi, wanda yanzu ta zama abin koyi.
Haka kuma, sun yabawa ƙudirin sa na gina sabuwar hanyar cikin gari (Township Road) da shataletale, wanda suka ce zai kara wa garin Dutsi kyan gani da bunƙasa tattalin arzikin yankin.
A yayin miƙa kyautar, al’ummar yankin sun bayyana cewa wannan karramawa alama ce ta gamsuwa da godiya, tare da tabbatar da ƙudirin su na ci gaba da goyon baya ga gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, da kuma shugaban ƙaramar hukumar Dutsi, domin ci gaban al’umma baki ɗaya.
A jawabin sa bayan da ya karɓi kyautar, shugaban ƙaramar hukumar Hon Kayawa ya godewa mutanen Dutsi bisa karamci da su ka nuna masa tare da alƙawarin cigaba da jajircewa wajen samawa ƙaramar hukumar ababen more rayuwa.
Ya yaba ga yadda al’ummar ke zaune lafiya a tsakaninsu da kira a gare su da su cigaba da nuna wannan mutuntaka a tsakanin su.
