A gaggauta sakin ɗan jarida, Ɗan Uwa Rano ba tare da sharaɗi ba – CIPP

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Daraktan cibiyar kula da gaskiya da kare haƙƙin ’yan jarida wato Center for integrity and press protection Nigeria (CIPP), Olumide Adekunle, ya bayyana kamawa tare da tsare ɗan jarida Ibrahim Ishaq (Danuwa Rano), da ’yan sandan Kano suka yi a matsayin abin da ya saɓawa doka.

Ana zargin ɗan jaridar da laifukan da suka haɗa da ɓata sunan daraktan karɓar baƙi na gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, da kuma gudanar da tashar YouTube ta Ɗan’uwa Rano TV ba tare da samun amincewar hukumar NBC ba.

A cewar CIPP, hukumar NBC tana da hurumin kula da gidajen rediyo da talabijin ne kawai, ba tashoshin yanar gizo ko YouTube ba, inda cibiyar ta buƙaci ‘yan sanda da su gaggauta sakin Ɗan’uwa Rano, ba tare da gindaya wani sharaɗi ba.

By ukarofi