Yajin aikin PENGASSAN ya durƙusar da samar da fetur a Satumba – NUPRC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta ƙasa (NUPRC) ta bayyana cewa, adadin samar da ɗanyen mai a Nijeriya ya faɗi zuwa matsakaicin ganga miliyan 1.581 a kowace rana a watan Satumbar 2025 a sakamakon yajin aikin da aka gudanar a fannin.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar ta hannun mai magana da yawunta, Eniola Akinkuotu, an bayyana cewa wannan koma baya ya samo asali ne daga yajin aikin kwana uku da ƙungiyar Ma’aikatan Mai da Iskar Gas (PENGASSAN) ta gudanar, wanda ya jawo rufe wasu muhimman cibiyoyin samar da mai da tashoshin fitarwa.

Haka kuma hukumar ta ce aikin gyaran kayayyakin tace mai da aka tsara a wasu manyan wurare biyu ya taimaka wajen ƙara rage yawan samarwa a watan.

A cewar bayanan da aka fitar, adadin ganga miliyan 1.581 da aka samar ya haɗa da ganga miliyan 1.39 na man ɗanye da kuma ganga 191,373.

Sanarwar ta ce, “A watan Satumba masana’antar ta samar da jimillar ganga miliyan 47.43 na ɗanyen mai, abin da ke nuna ƙaruwa da kashi 1.61 cikin ɗari idan aka kwatanta da makamancin lokaci a bara.”

Wannan, a cewar NUPRC, ya nuna ɗan ƙaramin ci gaba idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.55 da ake samarwa a watan Satumba na shekarar 2024 — alamar cewa ana samun ƙarin ci gaba a hankali.

Sai dai kuma hukumar ta ce idan aka kwatanta da watan Agusta 2025, an sami raguwa da kashi 3.09 cikin ɗari, domin a wancan lokaci an samar da ganga miliyan 1.63 a rana.

Duk da wannan koma bayan, NUPRC ta bayyana cewa Nijeriya ta cimma kashi 93 cikin ɗari na adadin da ƙungiyar OPEC ta ware mata, wanda ya kai ganga miliyan 1.5 a rana.

A watan da ake magana a kai, an samu matsakaicin samarwa mafi girma da ya kai ganga miliyan 1.81 a rana, yayin da mafi ƙanƙanta ya tsaya a ganga miliyan 1.35.

Hukumar ta kuma bayyana cewa binciken da ta gudanar kan manyan nau’ikan mai guda takwas da ake samarwa a ƙasar ya nuna cewa Forcados Blend ya bayar da kashi 15.86% na jimillar samarwa, Bonny Light ya bayar da kashi 13.31%, ƙua Iboe kashi 9.88%, Escraɓos Light kashi 8.96%, Bonga Crude kashi 6.83%, Agbami Condensate kashi 4.94%, Erha Crude kashi 4.55%, yayin da Amenam Blend ya bayar da kashi 4.2% na jimillar samarwa.

Rahoton ya nuna cewa duk da matsalolin yajin aiki da gyaran injina, Nijeriya na ci gaba da matsowa kusa da cikakken biyan ƙa’idar OPEC, abin da hukumar ta ce yana nuna ƙarfin da masana’antar ke ƙoƙarin dawo da shi bayan jinkirin da aka fuskanta a baya.

By ukarofi