Iyalan da suka amfana da tallafin gwamnati sun kai miliyan takwas – Ministan Jinƙai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta raba fiye da Naira Biliyan 300 ga iyalai sama da miliyan takwas a faɗin ƙasar nan ta hanyar shirin Conditional Cash Transfer (CCT) — wani shiri da ke nufin rage talauci da inganta rayuwar al’umma.

ƙaramin Ministan Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Yusuf Tanko Sanunu, ne ya bayyana hakan a taron tattaunawa da aka gudanar a Abuja domin tunawa da Ranar Rage Illolin Bala’o’i ta Duniya, a ranar Litinin.

Sanunu ya ce, wannan ci gaba wani ɓangare ne na Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu, wanda ya mayar da hankali kan taimakon al’umma da bunƙasa ƙarfin su wajen fuskantar ƙalubale.

“A halin yanzu, sama da iyalai miliyan 8.1 ne aka kaiwa wannan tallafi, da jimillar kuɗi sama da naira biliyan 300, wanda ya taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya, ilimi da walwalar su,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati na shirin bayar da bashi mara ruwa da ba tare da jingina ba ga mutane 21,000 da ambaliyar ruwa ta shafa a sassa daban-daban na ƙasar nan.

“Za mu raba naira 300,000 ga kowane mutum cikin waɗanda bala’in ya shafa, domin rage asarar gonaki da farfaɗo da ayyukan noma,” inji Sanunu.

Haka kuma, ya bayyana wani shiri da ke haɗin gwiwa da Ma’aikatar Noma domin taimakawa ’yan gudun hijira ta hanyar samar musu da kasuwa mai tabbas ga amfanin gona da suke nomawa.

“A tsarin, gwamnati za ta sayi kashi 70 cikin 100 na amfanin da suka noma, sannan su riƙe kashi 30. Za a biya su kuɗin cikin lokaci don taimaka musu da kuɗin hannu,” in ji shi.

A nata jawabin, Daraktar Hukumar NEMA, Zubaida Umar, ta ce ƙasar na fuskantar ƙaruwa wajen yawan bala’o’i da tsaninsu, musamman sakamakon canjin yanayi, rikice-rikice, cututtuka da matsalolin fasaha.

Ta jaddada buƙatar gwamnati da masu ruwa da tsaki su koma ga tsarin da ke taimaka wa gabanin faruwar bala’o’i, ba wai jira sai sun faru ba.

“Dole mu koma tsarin da ke haɗa kuɗaɗe daga fannoni daban-daban domin gina juriya da shirin gaggawa mai ɗorewa,” inji ta.

Zubaida ta kuma bayyana ƙaddamar da sabbin tsare-tsare biyu na ƙasa — NEMA Strategy Plan (2025–2029) da National Disaster Risk Reduction Strategy (2025–2030) — waɗanda za su zama ginshiƙai wajen tsara ayyukan rage bala’o’i a Nijeriya.

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Benjamin Kalu, Gwamnan Zamfara Dauda Lawal, da wasu jami’an gwamnati da abokan hulɗa na ƙasashen waje.

By ukarofi