Daga MAHDI MUSA MUHAMMADl
Kungiyar Masu Binciken Harkokin Man Fetur Mai Zaman Kanta da ke ƙasar Ingila (IIP), ta ce ba ta samu wani hujja da ke nuna cewa Kamfanin Tace Mai na Dangote ya shigo da man fetur mara inganci cikin Nijeriya ba, tana mai bayyana irin waɗannan zarge-zargen a matsayin “marasa tushe, marasa ma’ana, kuma ba su da hujjar da za a iya tabbatarwa.”
A cikin wani rahoto da jagoran binciken ƙungiyar, Raymond Neil, ya sa hannu a kai a ranar Juma’a, IIP ta bayyana cewa binciken da ta gudanar kan bayanan jigilar kaya, takardun kwastom da kuma bayanan tace mai, ya nuna babu wani alamar da ke nuna cewa kamfanin ya shigo da fetur mai ƙunshe da sinadarin sulphur sama da ƙa’idar ƙasa wato 50 parts per million (ppm).
Neil ya bayyana cewa ƙungiyar ta fara binciken ne bayan rahotannin wasu kafafen yaɗa labarai da suka ce wani jirgin ruwa ya kawo man da ke da sanadarin sulphur mai yawa zuwa tashar Dangote ƙarƙashin suna na man da aka tace a gida.
Sai dai ya ce, binciken ya gano cewa kayan da ake magana a kai ba man fetur ba ne da aka gama tacewa, illa dai wani kayan haɗi ne da ake amfani da shi wajen ƙarin tacewa a masana’antar mai – abin da ke da halarta a duk faɗin duniya.
“Nazarinmu ya tabbatar cewa abin da aka kawo kayan haɗi ne, ba man da za a sayar kai tsaye ba,” inji Neil.
“An shigo da shi ne don inganta aikin tace mai, ba don sayar da shi ga jama’a ba. Don haka zargin cewa kamfanin Dangote ya shigo da man gurɓatacce ya saba da gaskiya da kuma tsarin kasuwanci.”
Ya ƙara da cewa, masana’antun tace mai a Turai da Asiya suna yawan shigo da irin waɗannan kayan kamar high-sulphur catalytic gasoline (HSCG) ko straight-run naphtha domin daidaita samarwarsu, kuma hakan ba yana nufin suna sayar da man gurɓatacce ba.
Rahoton IIP ya kuma tabbatar da cewa dukkanin takardun shigo da kayan kamfanin Dangote da izinin hukumomin Nijeriya — Hukumar Kwastom (NCS) da Hukumar Haƙowa da Tace Man Fetur (NMDPRA) — sun nuna bin ƙa’ida ne cikin tsarin shigo da kayan tace mai.
Haka kuma kamfanin na aiki ne ƙarƙashin lasisin yankuna masu haƙo mai bare da haraji ba, wanda ke nufin duk wani abu da aka shigo da shi dole ne a tace shi kafin ya shiga kasuwar cikin gida.
Neil ya bayyana cewa bincikensu ya haɗa da duban sakamakon gwajin dakin gwaje-gwaje, bayanan amfani da ƙarfin tacewa, da kuma takardun binciken da aka mika ga hukumomi a Ingila da Nijeriya.
Ya ce, babu wani shaida da ke nuna cewa kamfanin ya shigo da man da aka gama tacewa don sayarwa cikin gida.
“Matakin sanadarin sulphur da aka ambata yana cikin man haɗi, ba man amfani kai tsaye ba. Kamfanin Dangote yana da tsarin tacewa da ke rage sinadarin sulphur ta hanyar hydrodesulphurisation da sauran hanyoyin zamani,” inji shi.
Ya yi gargaɗin cewa yada bayanan ƙarya na irin wannan na iya rage amincewar jama’a da kamfanin, a daidai lokacin da Nijeriya ke ƙoƙarin inganta tace mai a gida.
IIP ta yaba wa kamfanin saboda yadda yake bin ƙa’idojin tsaro da nagarta na duniya, tana mai cewa “duk wani samfurin da ke fita daga masana’antar Dangote yana da takardar shaidar inganci daga dakin gwaji mai lasisin ISO.”
A ƙarshe, ƙungiyar ta ce za ta raba cikakken rahoton nata da hukumomin Nijeriya da ƙungiyoyin farar hula, domin tabbatar da cewa tattaunawa kan harkokin makamashi ta kasance bisa hujja da gaskiya, ba zato ba.
