Wani ɗan dambe daga ƙasar Masar mai suna Ashraf Mahrous ya jawo hankalin duniya bayan da ya ja jirgi mai nauyin tan 700 (kusan kilo 635,000) da haƙoransa a gaɓar tekun Hurghada da ke yankin Bahar Maliya.
Mahrous, wanda ake kira “Kabonga”, kuma aka fi saninsa da laƙabin “Jarumi Mai ƙarfi” a Masar, ya kuma ci gaba da jan wasu jiragen ruwa biyu tare da nauyin tan 1,150 (fiye da kilo miliyan ɗaya) gaba ɗaya.
“Na zo yau domin kafa tarihi a duniya,” inji Mahrous bayan gwajin. “Na jawo su duka, da taimakon Allah, domin in tabbatar wa duniya cewa Allah ya albarkace ni da ƙarfi fiye da kowa.”
Mahrous ɗan shekara 44, daga birnin Ismailia, ya bayyana cewa zai tura bidiyo da hotunan gwajin nasa zuwa kundin Guinness World Records domin a tabbatar da sabon nasarar da ya cimma — kasancewar tarihin da ake shi yanzu shi ne jan jirgin tan 614 a shekarar 2018.
A watan Maris da ya gabata, Mahrous ya kafa tarihi ta hanyar jan jirgin ƙasa mai nauyin tan 279 da igiya a cikin haƙoransa na tsawon mita 10, inda Guinness ta tabbatar masa da rikodin “heaɓiest rail pull” — wato jan jirgin ƙasa mafi nauyi a duniya. Haka kuma yana da takardun shaidar Guinness kan jan mota mafi nauyi a mita 100 da jan manyan karagon jirgin ƙasa mafi nauyi.
Tun a shekarar 2022, Mahrous ya shahara bayan ya ja mota mai nauyin kilo 15,730 da haƙoransa, abin da ya kafa masa suna a fagen nishaɗi da ƙarfi.
Don shiryawa wannan sabon ƙalubale, Mahrous ya sha horo na awanni shida a rana, yana cin abinci mai ɗauke da furotin — ciki har da ƙwai 12, kaji biyu, da kuma kilo biyar na kifi a rana.
Tauraron mai tsayin mita 1.9 (ƙafa 6 da inci 3) kuma mai nauyin kilo 155 (fam 341) ya ce tun yana ƙarami yake da ƙarfi, har ma ya taɓa karya hannun abokinsa yayin wasa da shi.
Yana da ƙwarewa a kung fu, kickboɗing da dambe, inda daga bisani ya kafa ƙungiyar dambe a birnin Kahira. Abokansa ne suka shawarce shi ya nemi kafa tarihiba duniya bayan sun gan shi yana juyar da babban tayar mota sau 10 a jere, kuma yana tura mota da yatsa guda.
Mahrous ya ce, ba ya amfani da magungunan ƙara ƙarfi, amma yana cin abinci, bacci, da motsa jiki sau biyu a rana.
