
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu ƙarin adadin jami’an tsaro a Birnin Tarayya Abuja a yayin da zanga-zangar lumana ta neman sako Nnamdi Kanu ta rikiɗe zuwa hargitsi a wasu sassa.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faro ne a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin dakatar da zanga-zangar ta ‘#FreeNnamdiKanu’, wadda ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Omoyele Sowore ya shirya.
An ruwaito cewa, jami’an sun watsa barkonon tsohuwa daga yankin Maitama har zuwa Transcorp, inda aka gargaɗi al’umma da su ƙaurace wa wuraren.
Haka kuma, an datse babbar hanyar da ke kaiwa zuwa yankin Federal Secretariat, inda dandazon jami’ai ke korar duk wanda ya yi yunƙuri bi ta titin.
Sannan, babu hanyar zuwa yankunan majalisa, kotuna da Fadar Shugaban Ƙasa.
Bugu da ƙari, akwai shingen bincike mai cike da jami’an sojoji da ƴan sanda a babban titin Kubwa.
Da fari, rundunar ƴan sanda ta gargaɗi masu shirin shiga sahun ƴan zanga-zangar da ke nema sakon jagoran na Biafra da kada su yi a yankin Fadar Shugaban Ƙasa da kewayenta.
