DA Ɗumi-Ɗumi: Nnamdi Kanu zai kare kansa a kotu bayan lauyoyinsa sun tsame hannu a shari’arsa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban lauyoyin da ke kare Nnamdi Kanu a kotu, wato Kanu Agabi, ya sanar da batun neman janye hannu a wakiltar tsararren jagoran na ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara (IPOB).

Ya ce, ya yi haka ne sakamakon miƙa buƙatar haka da Nnamdi Kanu ya yi a gare su bisa rashim gamsuwa da wakilcin nasu.

Akan haka ne baki ɗaya manyan lauyoyin (SAN) da ke cikin tawagar suka janye daga ƙarar, lamarin da Kanu ya tabbatar da bakinsa a kotu.

Shugaban na IPOB ya faɗa wa kotun cewa daga yanzu shi zai riƙa wakiltar kansa da kansa koda kuwa hakan ka iya sauyawa a nan gaba.

Da aka tambaye shi ko yana buƙatar a ba shi sabon lauyan da zai riƙa kare shi, sai ya ce ba ya buƙata, inda ya ƙara da cewa kotun ba ta da hurumin ja da shi akan lamarin shari’arsa.

Haka kuma, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar AAC kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya gana da Kanu a kotu, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

By Babaji