2027: Fitowa takarar Jonathan na tangal-tangal yayin da jagororin Neja-Delta suka goyi bayan sake zaɓen Tinubu

Spread the love

Rahotanni sun nuna cewa, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba mai tsanani domin ya janye daga zargin da ake yi na cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027, tare da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin neman wa’adi na biyu.

Wasu Majiyoyi sun shaida cewa, manyan fitattun ƴan yankin Neja-Delta ne ke jagorantar wannan matsin lamba, ciki har da tsohon shugaban ƴan tawayen yankin, Cif Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo.

Wasu daga cikin mutanen Jonathan na yankin Neja-Delta sun roƙe shi da ya ajiye duk wani shirin dawowa mulki, ya maida hankali wajen tallafa wa Tinubu domin samun nasara a wa’adinsa na biyu.

Majiyoyin sun ce, Tompolo ya ziyarci Jonathan a ranar 16 ga watan Oktoba a garin sa na Otuoke, ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, domin yin magana kai tsaye da shi kan wannan batu.

A cewar wata majiya mai tushe, taron ya kasance na siyasa, kuma ya mai da hankali wajen roƙon Jonathan da ya daina tunanin tsayawa takara a 2027.

Haka kuma, an ce Tompolo ya shaida wa tsohon shugaban ƙasar cewa yawancin mutanen yankin Neja-Delta ba su da ra’ayin ganin ya sake neman shugabanci.

By Babaji