Zargin sauya akalar kuɗaɗen jam’iyya: SDP ta dakatar da Shugabanta, Gabam da wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar SDP ta sanar da dakatar da Shugabanta na ƙasa, Shehu Gabam bisa zargin sa da hannu a almundahanan kuɗaɗe da sauya akalar kuɗaɗen jam’iyya.

Haka kuma, jam’iyyar ta dakatar da Oditanta na ƙasa, Nnadi Clarkson da Shugaban Matasa na ƙasa, Chukwuma Uchechukwu.

SDP ta sanar da haka ne ta Sakataren yada labaranta, Araba Aiyenigba a wata ganawa da manema labarai, inda ta ce hakan ya biyo bayan matsayar da kwamitin ayyukanta ya cimma a zamansa na ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.

A cewarsa, an fara dakatar da Gabam da wasu jami’ai biyu ne a ranar 24 ga Yuni 2025 saboda zargin rashin da’a da ɓarnar kuɗaɗe, sannan aka kafa kwamitin bincike a ranar 4 ga Yuli, wanda ya miƙa rahotonsa a 18 ga watan nan.

Aiyenigba ya ƙara da cewa bayan nazari da tantance rahoton, kwamitin zartarwa na ƙasa ya amince da korar jami’an da abin ya shafa, ciki har da Gabam, Ogbonna Uchechukwu, da wasu guda takwas, saboda shiga haramtacciyar hanya ta ƙwace takardu da kayayyaki daga hedkwatar jam’iyyar.

Ya ce, wannan hukunci zai fara aiki nan take, wato daga ranar Alhamis, 23 ga Oktoba 2025, kuma an ɗauki matakan tabbatar da tsabtace tsarin gudanarwa a jam’iyyar.

By Babaji