
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi bayanin dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauye-sauyen muƙamai a rundunonin sojojin Nijeriya ciki har da cire babban hafsan tsaro da naɗe-naɗen muƙaman sababbin jagororin tsaro.
Jawabin ya biyo bayan cecekuce da ake yi game da sauyin na kwatsam duba da yadda aka fitar da rahoton zargin Yuni juyin mulki daga wasu sojoji.
Amma duk da haka, Fadar Shugaban Ƙasar ta tirje akan lallai sauyin bai da alaƙa da hakan, saida abu ne da aka yi na dabarun tsaro da inganta ayyukan fannin a faɗin ƙasar.
A jiya Juma’a ne Shugaba Tinubu ya sanar da naɗin Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS), wanda ya maye gurbin Janar Christopher Musa.
Sauran jagororin da aka naɗa a wasu muƙamai sun haɗa Shugaban sojoji, wato Manjo Janar W. Shaibu; Shugaban sojojin sama AVM Aneke; RA I. Abbas wanda shi je sabon shugaban sojojin ruwa. Haka kuma akwai shugaban sashen Leƙen Asiri na hedikwatar tsaro Manjo Janar E.A.P Undiendeye, wanda ya cigaba da zama a muƙaminsa.
An yi sauyin ne kwanaki kaɗan da rahoton zargin yunƙurin juyin mulkin ya watsu a kafafen yaɗa labarai, lamarin da ya yi sanadiyyar kama wasu sojoji da hannu aciki, ikirarin da hedikwatar tsaron ta musanta.
Da yake jawabi ga manema labarai, Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, ya ce babu wata alaƙa tsakanin garambawul ga sojoji da zargin juyin mulki.
