Abinda ya sa mu ka kai Sowore kurkuku duk da samun beli – ‘Yan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda ta yi bayanin dalilin da ya sa suka tasa ƙeyar ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Omoyele Sowore zuwa gidan yarin Kuje jim-kaɗan da Kotun Majestare ta Abuja ta bada belinsa a jiya Juma’a.

Da fari, ƴan sanda sun kama Sowore ne a ranar Alhamis bisa tuhumarsa da tayar da hankalin al’umma da saɓa wa dokar lumanan bainar jama’a.

Hakan na zuwa ne bayan da ya shirya zanga-zangar neman sakin Nnamdi Kanu, wato tsararren jagoran ƙungiyar ƴan fafatukar kafa ƙasar Biafara, IPOB.

Daga bisani aka tsare shi tare da wasu mutane guda 12 ciki har da ɗan uwan Kanu, wato Emmanuel Kanu.

A yayin shari’ar ne bayan Sowore ya wanke kansa a kotun game da laifin da aka tuhumce shi a kai sai alƙali ya bada belinsa.

Kakakin ƴan sanda, Benjamin Hundeyin a wani rubutu ta kafar X, ya bayyana cewa an sake kama Sowore ne sakamakon rashin cika sharuɗɗan belin nasa.

Ya bayyana cewa, jami’ansu sun yi aiki ne bisa doka, wanda kuma yin hakan wani ɓangare ne na aikinsu, inda ya ƙara da cewa akwai takardar izinin tsare shi da ke nuna har sai ya cika sharuɗɗan beli kafin a sake shi.

By Babaji