Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wani masanin manufofin gwamnati kuma mai fafutukar ingantaccen shugabanci, Tijjani Sarki, ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya naɗa Farfesa Abdallah Uba Adamu a matsayin Shugaban Jami’ar Northwest, Kano na dindindin.
Ta cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa a aka rubuta ranar 25 ga Oktoba, 2025, Sarki ya bayyana Farfesa Adamu a matsayin “mabuɗi, haziƙin malami, shugaba mai hangen nesa wanda ya tabbatar da bajintarsa a harkar ilimi a Najeriya.”
Ya bayyana cewa Farfesa Adamu, ɗan asalin Kano da aka haifa a shekarar 1956, ya samu digirinsa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Jami’ar Landan, da Jami’ar Sussex, kuma ya zama Farfesa biyu a fannoni daban-daban – na Ilimin Kimiyya da Sadarwa da Al’adu a Jami’ar Bayero, Kano (BUK).
Sarki ya waiwaya baya da irin gagarumar nasarar da Farfesa Adamu ya samu lokacin da yake Shugabancin buɗaddiyar jami’ar ta ƙasa (NOUN) daga 2016 zuwa 2021, inda ya jagoranci sauye-sauye da dama kamar dawo da hedkwatar jami’ar daga Legas zuwa Abuja, ƙaddamar da tsarin karatu ta yanar gizo, da tsaurara ƙa’idojin ɗaukar malamai masu digiri na biyu wato Ph.D. kawai.
“Jagorancin Farfesa Adamu ya kawo sabbin dabaru, daidaito, da samar da kima a tsarin karatun buɗaddiyar jami’a a Najeriya,” in ji Sarki.
Ya kuma jaddada cewa gogewarsa a duniya — musamman lokacin da ya zama babban mai binciken fulbright a jami’ar California, Berkeley, da kuma ayyukansa tare da ƙungiyoyin duniya irin su WHO, UNICEF, da DFID — sun ƙara masa ƙwarewa a shugabanci da ilimi.
Kazalika, Sarki ya roƙi gwamnatin jihar da ta tabbatar da naɗa shugabanci bisa cancanta da gaskiya, yana mai cewa ƙwarewa da hangen nesa, da sahihancin Farfesa Adamu” sun isa su ɗaga martabar Jami’ar Northwest zuwa matakin manyan cibiyoyin ilimi a ƙasar.
Sannan ya ƙarkare da kira ga Gwamna Yusuf da ya ci gaba da tallafa wa ci gaban ilimi da kuma haɓaka ƙwarewar haziƙan jihar domin su taka rawar gani wajen ci gaban Kano ta fuskar ilimi da ƙirƙire ƙirƙire.
