Farfesa Muhammad Khalid Othman ya zama shugaban jami’ar FUDMA

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar gudanarwar na jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma ta amince ta daɗin Farfesa Muhammad Khalid Othman a matsayin shugaban jami’ar.

Shugaban hukumar gudanarwar na jami’ar HE.Ali Abubakar Jatau ya sanar da haka jim kaɗan da kammala taron hukumar gudanarwa na jami’ar karo na 36 da ya gudana a garin Dutse,a jihar Jigawa.

A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na jami’ar malam Nasiru Abdul ya fitar naɗin ya biyo bayan gabatar da rahoton haɗin gwiwa na zaben shugaban jami’ar.

Jatau ya ce fitowar Farfesa Othman matsayin shugaban jami’ar sai da hukumar gudanarwa ta bi duka ƙa’idojin gudanar da zaɓe da ya ƙunshi yan takarar kujerar shugaban jami’ar mutum 17.

Mutane 28 suka nuna buƙatar su na neman muƙamin shugaban jam’iyyar bayan akwai mutane uku da kwamitin ya gano suma suna nema.

Sabon shugaban jami’ar an haife shi a shekarar 1962 a ƙaramar hukumar Bindawa na jihar Katsina.

Kuma yayi karatun digiri na ɗaya da na biyu da na uku a jami’ar Ahmadu Bello Zaria har ya zama Farfesa kan harkokin noma.

Farfesa Muhammad Khalid Othman ya na da mata da ya’ya guda tara.

By ukarofi