Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sun haɗa da Shugabannin a KASROMA, KASEDA, Hukumar kula da ma’aikata da hukumar fansho.
Sanarwar ɗauke da sa hannun babban jami’in hulɗa da jama’a na gwamnan Muhammad kaula,Gwamnan ya umurce su da su tabbatar da aiwatar da ajandar wannan gwamnati na“Gina Makomar Ku”
Gwamnan ya amince da naɗin Injiniya Abba Junaidu MNSE a matsayin Shugaban hukumar gyaran hanyoyi ta Jihar Katsina (KASROMA).
Injiniya Junaidu yana da digiri na biyu (Master’s) a fannin gudanar da muhalli, da kuma digiri na farko (B.Eng) a Injiniyan gini. Ya yi aiki na dogon lokaci a matsayin Chief Building Officer da kuma mataimakin manajan ayyuka a ma’aikatar ilimi, tare da riƙe muƙaman Principal Civil Engineer da Chief Resident Engineer a ma’aikatar ayyuka.
Sai Dakta Babangida Ruma a matsayin darakta janar na hukumar kula da bunƙasa kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA).
Dakta Ruma, wanda ya taɓa zama mataimaki na musamman ga gwamna kan bunƙasa kasuwanci, masani ne a fannin fasaha, ɗan kasuwa, kuma mai fafutukar bunƙasa matasa. Hukumar UNESCO Institute for Information Technologies in Education ta bayyana shi a matsayin “Uban Fasaha da Kirkire-kirkire” saboda rawar da ya taka wajen amfani da fasaha domin ci gaban al’umma.
Bugu da ƙari, Idris Usman Tune zai shugabanci hukumar kula da ma’aikata (Civil Service Commission). Yana da digiri na farko a Siyasa (B.Sc Political Science), PGDPC, da MPPA. Tune ya riƙe muƙamai daban-daban a hukumomin gwamnati sannan ya kasance Shugaban ma’aikata na Jihar Katsina har zuwa Mayu 2023.
Gwamnan ya ƙara kafa hukumar fansho ta Jihar Katsina, inda Ibrahim Boyi Dutsinma ya zama shugaban hukumar na wucin gadi, Musa Rabiu Mahuta a matsayin darakta janar kan kuɗi da gudanarwa, Abbati Ibrahim Masanawa a matsayin darakta janar kan ayyuka, Usman Shehu a matsayin darakta janar kan ICT da gudanar da bayanai, sai kuma Dakta Faruk Aminu a matsayin mai kula da ayyuka daga waje (Independent Observer). Haka kuma wakilan MDAs da ƙungiyoyin ma’aikata za su haɗa kai da su bisa ga dokar gyaran fansho ta Jihar Katsina ta shekarar 2025.
A hukumar kula da fanshon ma’aikatan Jiha da ƙananan hukumomi (Pension Transition Board), Hon. Muntari Dan Ammani zai riƙe mukamin sakatare janar, yayin da Garba Sanda Mani, zai kasance shugaban hukumar na wucin gadi. Dr. Faruk Aminu zai ci gaba a matsayin mai sa ido daga waje, tare da wakilan MDAs da ƙungiyoyin ma’aikata.
Gwamna Raɗɗa ya umurci sabbin shugabannin da su mayar da hankali kan ingantaccen aiki ga al’ummar Jihar Katsina, bisa manufar gwamnatinsa ta “Gina Makomar Ku”.
Naɗin ya fara aiki nan take.
